Ci gaba cikin sauri da Sin ta samu cikin shekaru sama da 40 da suka gabata, sun zo da nasu illa: yayin da fitilu a yankin kogin Yangtze dake gabashin kasar ke haskaka sararin samaniya da dare, har yanzu kauyuka a yankin yammacin na amfani da kyandir. Za a iya ziyartar yankin Beijing da Tianjin da Hebei cikin rabin awa ta jirgin kasa mai sauri, amma har yanzu akwai wagegen gibi na ci gaba. Wannan gibi yana jinkirta saurin tafiyar, kuma zai iya haifar da matsaloli ga sauran sassa. Manufar dabarar hade aikin raya larduna ita ce, rage gibin dake tsakanin larduna da rage rashin daidaito da tabbatar da jama’a a dukkan larduna sun ci gajiyar ci gaba cikin daidaito, wanda ke nuna kokarin samun ci gaba da wadata cikin daidaito.
Ta hanyar hade aikin raya larduna, kasar Sin ta yi amfani da hikimar da aka gada cikin shekaru 5000 da suka gabata. Na farko shi ne, manufar tunanin aiki da hankali. Tsohuwar dabarar kasar Sin ta tafiyar da gwamnati ta nanata bukatar aiwatar da cikakken tsari, kuma yanzu gina babbar kasuwa ta bai daya da tsara layukan dogo masu saurin tafiya da suka ratsa juna misali ne na yadda ake aiwatar da wannan manufa da kuma yadda ake tafiyar da harkokin gwamnati.
- Matakin Sin Na Karfafa Takaita Fitar Da Abubuwa Masu Alaka Da Ma’adanan “Rare Rarth” Na Nuni Ga Aniyarta Ta Kare Tsaron Kasa
- ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zanga A Karkashin Jagorancin Sowore A Abuja
Na biyu shi ne zaman lafiya da hadin gwiwa. Tsarin shugabancin kasa na inganta zaman lafiya da hadin gwiwa da kawar da shingaye ta fuskar gudanar da mulki da rarrabuwa tsakanin yankuna, inda yake ware albarkatu a tare da yaki da gurbatar muhalli a tare da cin moriya tare. Akwai kuma tunanin rungumar yanayin wuri, kamar raya harkokin tattalin arziki na dijital a yankin gabashi da shuke-shuken hatsi kan gangare a yankin yammaci da sauya sansanonin masana’atu zuwa na zamani da sabon karfin samar da hajoji a arewa maso gabas da lalubo fifikon da suke da shi da raya masana’atun wurare da samun ci gaba mai inganci a kowanne yanki.
Muhimmin jigon dabarar raya yankunan a tare shi ne, bude kofar cimma zamanantarwa da samun wadata na bai daya ga dukkan jama’a. (Fa’iza)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp