Yanzu haka, an shafe mako daya ana fama da rikici tsakanin Palesdinu da Isra’ila, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane a kalla 3500. Kuma MDD ta yi gargadin cewa, halin jin kai na kara tsananta a zirin Gaza.
To ko mene ne ya sa rikicin sassan biyu ya ki karewa? Dalili mai tushe shi ne Palesdinawa ba su samu damar kafa kasarsu ba, wanda hakan ya kasance burinsu na dogon lokaci, shi ya sa suke cikin mawuyacin hali na rashin samun daidaito.
Rikicin da ya barke a wannan karo ya shaida cewa, kafa kasa daya kawai zai jefa wannan yanki cikin hali na fama da rikice-rikice babu iyaka, hakan ya sa manufar kafa kasashe biyu, ta zamo hanya daya tilo ta warware wannan matsala. Saboda amince da hakan, MDD da kasashen Larabawa, da Sin, da Rasha, da EU, da dai sauransu, sun yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su tsagaita bude wuta, da komawa teburin shawarwari, don tabbatar da zaman lafiya, da zama tare cikin lumana. Yankin Gabas ta tsakiya ba zai samu ainihin zaman lafiya ba, sai an tabbatar da wannan manufa daga tushe. (Amina Xu)