A ranar 18 ga watan Janairun shekarar 2017, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci babban taro a birnin Geneva na kasar Switzerland, inda ya gabatar da jawabi mai taken “Kiyaye makomar bai daya ga dukkan bil adama”, inda ya yi cikakken bayani a kan manufar makomar bai daya ta dukkan bil Adama, tare da sanar da shawarar kasar Sin ta fannin tinkarar kalubalen da ake fuskanta a zamanin da muke ciki.
A cikin wadannan shekaru biyar da suka gabata, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen kiyaye dunkulewar kasashen duniya da ma kiyaye cudanyar da ke tsakanin bangarori daban daban, a kokarin tabbatar da manufar nan ta kiyaye makomar bai daya ta dukkan bil Adam.
Philippe Monnier, tsohon shugaban hukumar raya tattalin arzikin yankin Berne na birnin Geneva, ya yi nuni da cewa, bunkasuwar kasar Sin da ma yadda kasar ke ta kara bude kofarta ga ketare, wani albishir ne ga tattalin arzikin duniya, ya ce, “Kasar Sin na kokarin sa kaimin dunkulewar kasashen duniya, baya ga rawar da take takawa a kungiyar dake kula da harkokin cinikayya ta duniya WTO, kuma hakan zai taimaka ga inganta mu’amala da ciniki a tsakanin kasa da kasa, tare da sa kaimin bunkasuwar tattalin arzikin duniya.” (Lubabatu)