Masharhanta da dama sun nazarci muhimman batutuwa da aka tattaunawa, yayin babban taron wakilan JKS na 20 da ya kammala a kwanan nan, tare da yabawa alkawuran da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ambata, cikin jawabinsa yayin ganawa da ’yan jaridu, lokacin kammalar taron na bana, musamman ma gabar da ya ambato aniyar kasar sa, ta kara fadada bude kofarta ga kasashen waje, tare da tabbatar da nasarar manufar zurfafa gyare-gyare a dukkanin fannoni, da samar da ci gaba mai nagarta.
Har ma ya sha alwashin cewa, Sin za ta samar da karin damammaki ga duniya.
Ko shakka babu, idan aka yi duba da irin gudummawa da kasar Sin ke bayarwa ga bunkasar tattalin arzikin duniya, hadi da yadda a yanzu shugabannin take kara tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da yin tafiya kafada da kafada da sauran sassan duniya, za a amince da cewa, ci gabanta zai kara fadada ci gaban duniya baki daya.
A matsayinta na kasa ta 2 mafi karfin tattalin arziki a duniya, Sin na da kasuwa mai yalwa, wadda ke kara jan hankulan duniya. Don haka ne ma masana ke ganin wannan manufa, ta kara bude kofa ga sassan duniya da Sin ta alkawarta, za ta tallafawa farfadowar tattalin arzikin duniya, tare da amfanar da al’ummun kasa da kasa.
Kawo yanzu, Sin ta zamo babbar abokiyar cinikayyar kasashe sama da 100, ta kuma kafa yankunan cinikayya maras shinge, tare da sanya hannu kan muhimman yarjeniyoyin cinikayya, irinsu cikakkiyar yarjejeniyar hadin gwiwar raya tattalin arziki ko RCEP, da dandalin raya hadin gwiwar Sin da nahiyar Afirka na FOCAC da sauransu.
Bugu da kari, Sin na taimakawa kasashe masu tasowa da musayar fasahohi, yayin da ayyukan da ake gudanarwa karkashin shawarar ziri daya da hanya daya, suka bude sabon babi ga raya cudanyar cin moriyar juna, tsakanin ta sasssan duniya daban daban. (Saminu Hassan)