Ganin yadda kullum ake kara samun wayewa, sakamakon bunkasar ilimin addini a wannan kasa, ya sa wadansu abubuwa da yawa ake tsaftace su wajen gudanar da su, domin wadanda ke yi su samu nutsuwa wajen wanin cewa abun da suke yi bai saba wa addini da kuma al’ada ba.
Umar Muhammad Gobir na daya daga cikin matasan da suka mike tsaye wajen ganin an samu ci gaba a fannin dirama ko wasan kwaikwayo a dukkan fadin kasar nan.
Kamar yadda Umar ya bayyana a zantawarsa da wailinmu a Abuja, ya nuna cewa lallai lokaci ya yi da ya kamata masu wannan sana’a ta dirama su hada kai ta yadda za su yi amfani da basirar da Allah ya ba su wajen kara fahimtar da al’umma a kan fanni rayuwa iri daban-daban.
Ya kara da cewa zuwa yanzu wannan kungiya tasu ta samu cikkaiyar karbuwa, musamman ganin yadda ta fito da wasu bayanai da al’umma suka dade suna fatan su ji irin wadannan bayanai daga masu ruwa da tsaki a kan wannan harka ta dirama.
Umar ya ce masu dirama sun sha fuskantar kalubale, saboda wasu daga cikinsu da suke bata-rawarsu da tsalle, amma yanzu saboda ilimi da wayewa da kuma daukar dirama a matsayin sana’a ta sa ake kara mutunta masu wannan sana’a wanda hakan ke kara musu karfin gwiwa wajen kiyaye addini da al’adar kowace al’umma.