Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, manufofin kasar Sin na bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida sun amfana wa Sin da ma duniya duka, baya ga kara bunkasa tattalin arzikin Sin, sun kuma samar da muhimmiyar gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya.
A yau da safe, mataimakin firaministan Sin Liu He da sakatariyar baitulmalin Amurka Janet Yellen suka tattauna ta kafar bidiyo.
Game da wannan batu, Zhao Lijian ya bayyana cewa, Sin ta gano akwai wani labarin da aka bayar wai Sin ta gudanar da ayyuka ba na ciniki da ba na kasuwa ba, kalaman na Amurka babu kamshin gaskiya a cikinsu.
Zhao Lijian ya yi nuni da cewa, alkaluma da aka samu a shekaru fiye da 40 da suka gabata, sun nuna cewa, Sin ta cimma nasarar bunkasuwar tattalin arziki sakamakon manufofinta na bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a gida cikin nasara, da kuma yin amfani da tsarin kasuwa da tsarin taimakon gwamnati, dukkansu kwarewa ne da Sin ta samu wajen bunkasa tattalin arziki. (Zainab)