A daidai lokacin da Nijeriya ta shiga 2023, shekarar da za a gudunar da babban zabe wanda zai sa a samu sabon shugaban kasa daga ‘yan takara, al’amurar siyasar da dama sun wakana wanda kasar ba ta taba ganin irinsa ba tun lokakacin da aka dawo mulkin dimokuradiyya a 1999. Abubuwa da dama sun turnuke siyasar 2022 wasu na dadi, yayin da wasu akasin haka. Ga kadan daga ciki kamar haka:
Shekarar Ce Aka Gwabza Tsakanin Majalisar Zartarwa Da Majalisar Dokoki
Ba kamar shekarar 2021 ba wanda ayyukan ‘yan majalisar sun kasance masu sauki kuma zauren majalisa ya kasance cikin natsuwa da karancin ra’ayoyi, sai dai an samu akasin haka a shekarar 2022.
Duk da haka, zauren majalisa ya kasance mai ci ke da tarin batutuwa wanda ake kokarin magancewa, musamman wadanda suka shafi tsaro da kuma wasu al’amura wadanda suka danganci majalisar zartarwa.
A shekarar ce aka samu sa-in-sa na farko lokacin da shugaban kasa ya rattaba hannu kan kasafin kudin 2022 na naira tiriliyan 17.13, wanda ya bambanta da kasafin kudin da aka gabatar na naira tiriliyan 16.3.
Lokacin da shugaban yake rattaba hannu kan kasafin kudin ya yi la’akari da canje-canje ga tsarin kasafin kudi na asali a cikin sabbin abubuwan da aka shigar, inda ya cire wasu gaba daya, yayin da wasu ya rage kudaden da aka kasaftawa ga ayyukan, ya rage manyan ayyukan guda 10,733 da kuma gabatar da sabbin ayyuka 6,576 a cikin kasafin kudin.
Daya daga cikin manyan batutuwa dai shi ne, ‘yan majalisar dokokin Nijeriya guda 469 da suka hada da majalisar dattawa da majalisar wakilai sun sanya sama da sabbin ayyuka 6,000 cikin kasafin kudin da ya gabatar a watan Oktoba.
“Bukatar samar da manayan ayyuka guda 10,733 sun ragu, yayin da majalisar a gabatar da sabbin ayyuka 6,576 a cikin kasafin kudin,” Buhari ya fada haka a cikin jawabinsa.
Daga baya a watan Fabrairu, shugaban ya bukaci majalisar kasa ta cire ayyukan da kudinsu ya kai na naira biliyan 887.99 daga kasafin kudin 2022, sannan kuma a sake gabatar da kasafin kudin a watan Afrilu.
Rikici ya sake kaurewa a tsakanin majalisar zartarwa da majalisar dokoki lokacin zartar da gyarar dokar zabe na 2022.
Yayin da yake rattaba hannu kan dokar zabe na 2022 a ranar 25 ga Fabrairu, Shugaba Buhari ya koka da cewa tanadin ya zama babban lahani ga kasa, yana mai cewa yana janyo sabani ga sanannun abubuwan da tsarin mulki ya samar.
Ya ce sashe na 84 (12) ya zama rarrabuwar kawuna ga hana masu rike da mukaman siyasa kada kuri’a ko kuma a zabe su wani mukami a babban taron kowacce jam’iyya.
Sashin ya tanadi cewa, “Babu wani mai rike da mukamin siyasa a kowane mataki da za a zaba a matsayin wakili ko a zabe shi a babban taron kowacce jam’iyyar siyasa.”
Shugaban ya lura cewa sashin ya gabatar da cancanta da kuma ka’idojin rashin cancantar da ke matukar tasiri ga kundin tsarin mulki ta hanyar shigo da takunkumin rashin cancanta.
Amma nan take majalisa ta ki amincewa da gyaran da shugaban kasar ya gabatar. Sau da yawa a cikin maganganunsa kan lamarin, Kakakin Majalisar Wakilai, Hon Benjamin Kalu ya ce, “Muna son bayar da matakin da ba shi da alaka da ma’aikatan gwamnati. Sashi na 318 na kundin tsarin mulki ya bayyana waye ma’aikacin gwamnati, bai hada da mai rike da mukamin siyasa ba, don haka muna bukatar sanin abin da dokar zabe ke kokarin yi game da abin da aka shigar da shi. Dokar zabe ta yi magana a kan mukamin siyasa, yayin da kundin tsarin mulki ya yi bayani a kan ma’aikacin gwamnati.”
Haka kuma ya kara da cewa majalisa tana kokarin tabbatar da sahihin tsarin zabe, abin lura shi ne, ana amfani da mukamin siyasa a lokacin babban taron jam’iyya.
“Yana da mahimmanci a sanar da ‘yan Nijeriya su sani cewa majalisar dokoki tana tunani da kuma niyyar sake tsarin sahi na 84 (12). Dole ne ya zama an samu ingantaccen zabe, idan kowane daya daga cikin abubuwan ya bace zai shafi sauran gaba daya, wannan shi ne dalilin da ya sa muke son magance matsalar rike mukaman siyasa wadanda ake amfani da shi a matsayin kayan aiki yayin babban taron jam’iyya na kakaba dan takara. Yana da muhimmanci tsarin ya tuna da wadanda suke zaune a kasashen ketare,” in ji shi.
Sashe na 84 (8) ya tanadi cewa, “Jam’iyyar siyasa wacce ta amince da tsarin zaben fid da gwani na kai-tsaye don zaben dan takararta za ta fito fili a cikin kundin tsarin mulkinta tare da yin amfani da tsarin wajen zaben wakilan dimokuradiyya a babban taronta.”
Lokacin da aka gano kuskure, ‘yan majalisa sun kira ganawar gaggawa domin yin gyaya, inda suka gudanar da karatu na farko da na biyu da na uku duk a rana daya kan kudurin.
Mai tsawatarwa na majalisa, Yahaya Danzaria wanda shi ne ya kira ganawar gaggawan ya bayyana cewa ‘yan majalisa za su gyara kurakuran da ke cikin dokar zaben 2022.
Daga karshe, Shugaba Buhari ya hau kujeran na-ki wajen kin amincewa da gyara kudurin tare da siffanta lamarin da taron zaman shan shayi.
INEC Da Dokar Zabe
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kudurin dokar zabe da aka sake gyarawa wanda ya zama doka. Shugaban kasan ya rattaba hannu ne a ranar Alhamis 25 ga watan Fabrairu a fadarsa da ke Abuja, a gaban shugaban majalisan dattawa, Ahmad Lawan da shugaban majalisan wakilai, Femi Gbajabiamila da sauran jami’ai.
Kafin ya rattaba hannun, shugaban kasa ya bukaci majalisar kasa ta goge sashi na 84 (12) na kudurin dokar.
Zaben Jihar Ekiti
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana dan takarar jam’iyyar APC, Biodun Oyebanji a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar Ekiti.
Kwamishinan zaben, Farfesa Kayode Adebowale wanda ya kasance mataimakin shugaban jami’ar Ibadan shi ne ya sanar da sakamakon zaben.
Adebowale ya ce, “Oyebanji shi ne ya samu yawan kuri’un da aka kada, domin haka shi ne ya lashe zaben, sannan kuma shi ne zababben gwamnan Jihar Ekiti.”
Jam’iyyar APC ta samu kuri’u 187,057 wanda ta doke takwaranta ta jam’iyyar SDP da ta samu kuri’u 82,211, sai PDP da ta samu kuri’u 67,457 da kuma sauran jam’iyyu 13 da suka fafata a zaben gwamnan jihar da ya gabata a ranar Asabar.
Zaben Jihar Osun
Hukumar INEC ta ayyana Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar Osun.
Kwamishinan zaben Osun, Oluwatoyin Ogundipe shi ya bayyana sakamakon zaben da sanyin safiyar Lahadi, inda ya ce dan takarar PDP ya yi nasara da kuri’u 403,371. Ya dai kayar da dan takarar APC gwamna mai ci, Gboyega Oyetola wanda ya samu kuri’u 375,027 a zaben.
Batun Na’urar Tantance Masu Zabe (BBAS)
Hukumar INEC ta fuskanci kalubale wajen yin aiki da naurar tantance masu zabe, inda ta tabbatar da cewa tana aiki domin kawar da wadannan kalubale da ta fuskanta.
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu shi ya bayar da wannan tabbaci a wurin wata ganawa da kwamishinonin zabe da ya gudana a Abuja.
Shugaban INEC ya ce tun da an samar da naurar tantance masu zabe zai saukaka wa masu sanya ido wajen samun sahihin sakamakon zabe.
Ya ce “Lallai mun samu kalubale na rashin aikin yin wasu na’urorin, amma muna aiki a kai.”
INEC Ta Kaddamar Da Shawarwarin Masu Sa Ido Daga Zaben 2019
Hukumar INEC ta bayyana cewa ta kaddamar da mafi yawancin shawarwari da masu sa ido suka bayar bayan kammala zaben 2019.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu shi ya bayyana hakan lokacin da yake tarbar wakilan Kungiyar Turai (EU) masu saka ido kan zabe karkashin jagorancin Maria Arena a shalkwatan INEC da ke Abuja.
Ya ce bayan kammala zaben 2019, hukumarsa ta yi nazari kan rahoton da masu saka ido na cikin gida da na kasashen ketare suka ba ta, inda ta kaddamar da shawarwari guda 178.
Sabuwar Rajistar Zabe Da Aka Yi Wa Mutum 93,522,272
A ranar 26 ga watan Oktoban 2022, Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa a cikin sabon rajistar zabe an samu adadin mutum 93,522,272. Ya dai bayyana hakan ne lokacin ganawar hukumar na watannin hudun shekara tare da shugabannin jam’iyyu da ya gudana a shalkwatan INEC da ke Abuja.
Fitar Da Sunayen ‘Yan Takara
Bisa jaddawalin ayyukan babban zaben 2023, hukumar INEC ta fitar da sunayen ‘yan takarar shugaban kasa da gwamnoni da ‘yan majalisar dattawa da na wakilai a dukkan fadin kasar nan.
Za dai a gudanar da babban zaben Nijeriya ne a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, wanda za a zabi shugaban kasa da mataimaki da kuma mambobin majalisar dattawa da na wakilai.
Haka kuma a 2023 za a gudanar da zaben gwamnonin jihohi 31 cikin 36 da ke fadin Nijeriya. Ban da guda uku, amma dukkan sauran jihohin za a gudanar da zaben gwamna a ranar 11 ga watan Maris tare da zaben mambobin majalisar dokokin na jihohi bayan mako biyu ga zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa. Sai dai za a gudanar da zaben gwamna a jihohin Imo da Kogi da kuma Bayelsa a ranar 11 ga watan Nuwamba.
An Farmaki Ofisoshin INEC Sau 50 Tsakanin 2019 Zuwa 2022
Hukumar INEC ta bayyana cewa an farmaki ofisoshin INEC sau 50 a tsakanin 2019 zuwa 2022, wannan yana cikin rahoton LEADERSHIP.
Kakakin INEC, Mista Rotimi Oyekanmi shi ya bayyana hakan a cikin rahoton LEADERSHIP na mako mai taken ‘Lokutan da aka farmaki ofisoshin INEC tsakanin 2019 zuwa ranar 12 ga watan Disambar 2022.”
“Wadannan farmakin sun faru ne sakamakon rikice-rikicen zabe, zanga-zangan da bai da alaka da zabe da ayyukan ‘yan ta’adda kuma na ‘yan bindiga.
“Jerin farkamin ban da wadanda kayayyaki suka lalace sakamakon gobara da wasu iftila’i da suka hada da ambaliyar ruwa, mummunan iska, sacewa ko lalata kayayyakin zabe sa’ilin gudanar da zabe, sata da kuma farmakin jami’ai lokacin zabe,” in ji Rotimi.
Jam’iyyar PDP
Babban jam’iyyar adawa ta PDP ta shiga cikin rikici a 2022 wanda har yau an kasa dinke bakin zaren.
Rikicin Tsarin Karba-karba
A shekarar 2022, PDP ta fada cikin rikici dangane da yankin da za a bai wa tikitin takarar shugaban kasa a zaben 2023. Muhawara kan tsarin karba-karba ya turnuke ne lokacin da gwamnonin kudanci ciki har da wasu daga cikin jiga-jigan PDP suka dage dole sai mulki ya koma yankin kudu bayan karewar wa’adin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na shekaru takwas a matsayinsa na dan arewa.
Amma wasu daga cikin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar musamman daga yankin arewa sun dage cewa dole yankin arewa ne zai fitar da shugaban kasa kamar yadda tsarin jami’iyyar ke jujjuya mukamai.
Daga karshe, kwamitin mai mambobin 36 da jam’iyyar ta kafa karkshin jagorancin gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom ya bayar da shawarar a bari tikitin takarar shugaban kasa ga mai rabo. Kwamitin gudanarwa na PDP ya amince da wannan shawarar.
A watan Mayu, kwamitin gudanarwar PDP ya zayyano jerin abubuwan da suka faru wadanda ke haifar da rashin nasara da tashin hankali a cikin jam’iyyar.
Rikicin Tsauar Da Dan Takara Daga Arewa
Bayan rushe bin tsarin karba-karba, an samu ‘yan takara 17 wadanda suka sayi fom din takara a watan Afrilu. A cikin ‘yan takarar sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da kuma tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Anyim Pius Anyim.
Sauran sun hada da gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed da gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike da gwamnan Jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel da tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi da tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose da shahararren likitan da ke kasar Amurka, Nwachukwu Anakwenze da kuma Dele Momodu.
Haka kuma akwai, Mohammed Hayatu-Deen da masanin magunguna, Sam Ohuabunwa da tsohon shugaban majalisan dokokin Jihar Abiya, Cosmos Ndukwe da Charles Ugwu da Rt Hon Chikwendu Kalu da kuma mace guda daya tilo, Oliber Tareila Diana. An dai dakatar da ‘yan takara guda biyu.
Sai dai yunkurin ganin rashin tsayar da dan takara dan arewa ya ci tura, domin ‘yan takara daga arewa sun ki bayar da kai bori ya hau.
Yayin da Atiku ya ki amincewa da batun, haka kuma Saraki da Tambuwal da kuma Hayatudeen sun yi watsi da shawarar da shugaban kungiyar dattawan arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya bayar na fitar da mutum biyu daga arewa, wanda suka hada da Saraki da Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi, a matsayin ‘yan takara da za su wakilci yankin arewa a karkashin jam’iyyar PDP a zaben fid da gwani.
Abin takaici dai shawarar ta tilasta wa Arewa Dattawa Taron Arewa (NEF) ta nisanta kanta daga batun, saboda rawar da Farfesa Abdullahi ya taka.
Nasarar Atiku A Matsayin Dan Takarar PDP
Bayan kammala zaben fid da gwani na jam’iyyar da ya gudana a ranar 28 ga watan Mayu, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya lashe zaben. Atiku ya samu kuri’u 371, wanda ya doke gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike wanda ya samu kuri’u 237.
Sauran ‘yan takaran sun sami kuri’u kamar haka, Bukola Saraki ya samu 70, Sam Ohuanbunwa ya samu daya, Anyim Pius Anyim ya samu 14, Udom Emmanuel ya samu 38, sannan Bala Mohammed ya samu kuri’u 20.
Sai dai gwamnan Jihar Sakkwato, Tambuwal ya janye takararsa tare da mara wa Atiku baya gabanin zaben, wanda hakan ya janyo rudani a cikin jam’iyyar, inda a wani faifan bidiyo shugaban jam’iyyar PDP, Dakta Iyorchia Ayu ya taya Tamuwal murna a matsayin jarumi na babban taron jam’iyyar ana tsaka da zaben fid da gwanin, wanda hakan ya harzuka wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar.
Rikicin Zaben Mataimakin Dan Takara
Duk da ziyarar da Atiku ya kai wa dukkan sauran ‘yan takarar bayan kammala zaben fid da gwani, zaban mataimakin takararsa ya janyo sabon rikici a jam’iyyar.
An dai zayyano sunayen gwamnonin PDP daga kudu guda uku da ake tsammanin daya daga ciki zai iya zama abokin takararsa, wadanda suka hada Nyesom Wike na Jihar Ribas da Sanata Ifeanyi Okowa na Jihar Delta da kuma Udom Emmanuel na Jihar Akwa Ibom. Kwamitin shugabannin jam’iyyar masu taimakawa wajen zaben mataimakin kashi uku sun zabi Wike.
Atiku ya yi watsi da ra’ayin kwamitin inda ya dauki Okowa, wanda hakan ya fusata wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar.
Ballewar Gwamnonin G5 Da Atiku Da Ayu
Ba da jimawa ba bayan zaben mataimakin takara a PDP, sabon rikici ya sake kunno kai a cikin jam’iyyar, inda Wike da wasu shugabannin jam’iyyar suka raba gari da shugaban jam’iyyyar, Ayu tare da kiran ya sauka daga mukaminsa domin a bai wa dan yankin kudu. Mun kalubalanci cewa bai kamata dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar da shugaban jam’iyyar su kasance a yanki daya ba.
Wike ne ya fara gudanar da gangamin sai Ayu ya sauka daga kan mukaminsa tare da zargin sa da cin hanci a cikin kadaden jam’iyyar. Ayu ya musanta duk wata alaka da cin hanci da rashawa.
Abubuwan sun kara tsami ne lokacin da mambobin kwamitin gudanarwa na PDP suka zargi Ayu da bayar da cin hanci ga mambobinsu, saboda su wanke shi kan zargin da ake masa.
Mambobin kwamitin guda shida sun fito ne daga yankin kudu, inda suka ce sun dawo wa jam’iyyar kudaden da aka ba su na cin hanci da suka kai naira miliyan 28 zuwa naira miliyan 36. Daga baya mambobin sun gane cewa kudaden da aka ba su a matsayin kudaden hayansu ne na shekaru biyu.
Amma sauran mambobin kwamitin sun kalubalanci abokansu cewa kudaden suna kan tsarin doka.
A daidai lokacin da Atiku yake cewa cire Ayu bai cikin tsarin kundin jam’iyyar, kwamitin zartarwa na PDP ya gudanar da zaben raba gardawa kan Ayu.
Atiku da gwamnonin PDP sun gudanar da ganawar ta yadda za a magance rikicin jam’iyyar kafin zabe, amma lamarin ya ci tura.
Rikicin Jam’iyyar ADC
A cikin shekarar 2022 ce, jam’iyyar ADC ta fada cikin rikici bayan da Dumebi Kachukwu ya zama dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar.
Wani bangare na jam’iyyar ya dakatar da Kachukwu, amma an kori shugaban jam’iyyar ADC na kasa, sannan Sanata Patricia Akwashiki ya zama shugaban jam’iyyar na kasa. Tun daga lokacin abubuwa ba sa tafiya daidai a cikin ADC.
Kwankwanso Da NNPP
A cikin shekarar lokacin da jam’iyyun siyasa ke kokarin gudanar da babban taronsu, tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwanso wanda a bayan ya bar jam’iyyar PDP ya shiga APC, ya koma jam’iyyar NNPP domin samun burinsa na zama dan takarar shugaban kasa.
A cikin rahon mako-mako na LEADERSHIP, Kwankwanso ya samu goyon bayan wasu jam’iyyu ciki har da AP, amma daga baya shugabanta ya karyata wannan batu tare da yin ikirarin mulki ya koma kudu.
Kwankwaso ya ziyarci yankin kudu maso gabas na ganin cewa NNPP ta samu nasara a can. Ya samu tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar bayan lokacin da ya zama shugaban jam’iyyar a cikin makonni kalilan.
Mutane da dama sun shiga NNPP bayan da suka yi rashin nasara a zaben fid da gwani a sauran jam’iyyu, abokin hamayyarsa na siyasa kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya hade da Kwankwanso, amma sakamakon rikicin shugabanci da ya shiga tsakaninsa da Kwankwaso duk da an ba shi takarar sanata na yankin Kano ta tsakiya a NNPP, Shekarau ya raba gari da Kwankwaso tare da komawa PDP.
An dai so a yi kawance tsakanin Kwankwanso da Peter Obi na jam’iyyar LP, amma daga karshe lamarin ya ci tura, saboda Kwankwanso da Obi kowannan su ya ki amincewa ya zama mataimakin dan takara.
Tafiyar Siyasar ‘Yan ‘Obidient’
Tafiyar siyasar Peter Obi da mataimakin takararsa, Yusuf Baba-Ahmed da ake kira da ‘Obidient Mobement’ ta kawo sabon salo a cikin harkokin siyasan Nijeriya.
Tun dai lokacin da Peter Obi ya fice daga PDP ya samu takarar a LP a Uyo, aka samu gagarumin sauyi a cikin harkokin siyasar Nijeriya.
An dai ga yadda tafiyar Obidient ke kara kayatar da siyasar Nijeriya, wanda ta sa ‘yan saiyasa a yanzu haka ke ta tallan siyan kuri’u.
Kamar yadda wasu ‘yan siyasa suke fadin cewa Peter Obi ya kasance dan siyasan da bai da tsari, amma yana samun goyon baya fiye da sauran ‘yan takara a kafafan yada labarai.
Farfado Da Jam’iyyar SDP
Jam’iyyar SDP wacce aka kafa tun zamanin Moshood Abiola, ta dawo da rai ne lokacin da Yarima Adewole Adebayo ya shiga cikin masu neman takarar shugaba kasa.
Adebayo wanda ya kasance lauya mamallakin jidan talabijin na Kaftan TB, ya shiga cikin sahun masu neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar SDP, wanda hakan ya kara turnuke siyasar Nijeriya a 2022.
An dai samu abun mamaki ne lokacin da Shehu Gabam ya sauya ofishi daga sakataren SDP na kasa zuwa shugaban jam’iyyar na kasa.
Haka kuma, Dakta Olu Ogunleye ya yarda ya sauka daga shugabancin jam’iyyar na kasa zuwa sakatare. An yi duk wannan ne domin bai wa jam’iyyar damar samun dan takarar shugaban kasa daga kudu.