Bisa gayyatar da gwamnatin Najeriya ta yi masa, wakilin shugaba Xi Jinping na musamman kuma mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Peng Qinghua, ya halarci bikin rantsar da sabon shugaban Najeriya Bola Tinubu a Abuja, fadar mulkin Najeriya a ranar 29 ga watan Mayu. A jiya ne kuma shugaba Tinubu ya gana da Peng Qinghua a fadar shugaban kasa.
Peng Qinghua ya mika sakon taya murnar shugaban kasar Sin Xi Jinping ga shugaba Tinubu, inda ya ce, tun bayan kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu fiye da shekaru hamsin da suka gabata, a ko da yaushe kasashen Sin da Najeriya suna tsayawa tsayin daka kan huldar abokantaka na gaskiya, da taimakon juna, da hadin gwiwar samun nasara tare, da yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu, kuma dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta samu ci gaba matuka.
Ya bayyana cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da sabuwar gwamnatin Najeriya, wajen inganta dabarun raya kasa, da karfafa mu’amala a dukkan sassa, da tabbatar da goyon baya ga juna, da fadada hadin gwiwa a dukkan fannoni, da sa kaimi ga raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Najeriya zuwa mataki na gaba.
A nasa jawabin, shugaba Tinubu ya mika godiyarsa ga takwaransa na kasar Sin shugaba Xi Jinping, bisa aiko da wakilinsa na musamman don halartar bikin rantsar da shi, ya kuma bukaci Peng Qinghua da ya mika sakon gaisuwarsa ga shugaba Xi Jinping, yana mai cewa, Najeriya da Sin suna da ra’ayi iri daya, wajen gudanar da mulkin kasa, kuma ya kamata bangarorin biyu su karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu.
Ya ce bangaren Najeriya na son kara karfafa hadin gwiwa da bangaren kasar Sin, a fannonin tattalin arziki, da kasuwanci, da tsaro, ta yadda za a ciyar da alakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi. (Mai fassarawa: Ibrahim)