Kungiyar kwallon kafa ta Marseille da ke kasar Faransa ta kori mai horar da ‘yan wasan kungiyar Gennaro Gattuso bayan shafe watanni hudu kacal a matsayin kocinsu.
Gattuso ya jagoranci kungiyoyin Ac Milan, Napoli da Valencia kafin ya koma kasar Faransa domin ci gaba da jan ragamar Marseille wadda ya bari a matsayi na 9 akan teburin gasar French Ligue 1.
Marseille ta ayyana raba gari da Gattuso bayan ya jagoranci wasanni 15 inda ya yi nasara a wasanni 5 ya buga canjaras 5 inda ya yi rashin 5 jimilla.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp