A ranar Juma’a ne ’yan uwa Musulmi almajiran Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky, waɗanda aka fi sani da mabiya Shi’a a Nijeriya suka bi sahun ‘yan uwan su a duniya wajen gudanar da jerin-gwano don tunawa da masallacin Ƙudus.
An gudanar da wannan jerin gwano a kusan duk manyan biranen ƙasar nan, wanda ya haɗa da Kaduna.
Ana yin jerin-gwanon duk shekara-shekara ne na goyon bayan Falasɗinawa da ake gudanarwa a ranar Juma’ar ƙarshe ta watan Ramadan don nuna goyon baya ga Falasɗinawa da adawa da Isra’ila da yahudawan sahyoniya.
Ana kuma gudanar da ranar Qudus a wasu ƙasashe da dama musamman a ƙasashen Larabawa da sauran ƙasashen Musulmi, inda ake gudanar da zanga-zangar nuna adawa da mamayar da Isra’ila ke yi a gabashin birnin Ƙudus. Ana gudanar da taruka a ƙasashe daban-daban na al’ummar Musulmi da ma waɗanda ba Musulmi ba a duniya.
A shekarar 1979 aka fara yin wannan jerin-gwano a ƙasar Iran.
A jawabin da wakilin mabiya Shi’a a Kaduna Kaduna ya yi, Sheikh Aliyu Tirmizi, ya ce, “mun fito ne domin nuna adawarmu ga gallaza wa al’ummar Falasɗinu da kuma mamayar da Isra’ila ke yi a birnin Ƙudus, wanda muka saba fitowa a duk ranar Juma’ar ƙarshe ta watan Ramadan.”
Sheikh ɗin ya kushe abubuwan da ke faruwa a ƙasar Falasɗinu, harda dawo da masallacin Al-Aqsa birnin Qudus da kuma cigaba da kashe Falasɗinawa da ƙasar Isra’ila ta ke yi.
Malamin ya ƙara da cewa, “muna fitowa ne cikin tsari, amma a wasu lokuta jami’an tsaro su kan far mana babu gaira, babu dalili, inda a bara sai da suka kashe mana mutane da dama. A bana ma sun far mana da hayaƙi mai sa hawaye tare da harba harsasai masu rai, inda suka harbi sama da mutum 20”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp