A ranar Laraba ne masana da jami’ai daga kasashen Sin da Tanzania suka halarci wani taron karawa juna sani, inda bangarorin biyu suka yi alkawarin inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa
Taron na yini guda mai taken “Nyerere, kasar Sin da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa: Abota, hadin kai, da samun ci gaba tare,” an yi shi ne a birnin Dar es Salaam babban birnin kasar Tanzania a taron kaddamar da cibiyar Julius Nyerere da Kungiyar Nazarin Harkar ‘Yanci ta Afirka.
Shugaba kuma babban jami’in cibiyar kula da manufofin kasa da kasa ta Afirka ko CIP-Afrika a takaice, Omar Mjenga a taron na karawa juna sani ya ce, “Sin da Afirka sun ci gaba da marawa juna baya da hadin gwiwa, kuma ko shakka babu za su yi la’akari da wata sabuwar hanyar bunkasuwarsu don samun ci gaban zamani da wadata tare.”
Ya ce, babu wata kasa da za ta iya tinkarar manyan kalubalen da bil’adama ke fuskanta ita kadai, yana mai cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka na da muhimmanci. (Yahaya)