Jiya ne, aka kaddamar da girbin nau’in masara mai inganci dake samar da masara mai tarin yawa da aka samu ta hanyar wani bincike na hadin gwiwa, tsakanin masana kimiya na kasashen Sin da Kenya, a gabar da ake saran cewa, hakan zai taimaka wajen magance matsalar karancin abinci dake damun kananan manoma a yankin.
David Mburu, wani malami a kwalejin nazarin aikin gona da albarkatun kasa a jami’ar koyon aikin gona da fasaha ta Jomo Kenyatta (JKUAT), ya bayyana cewa, masu bicike na kasashen biyu, sun yi nasarar gano wani nau’in masara na gida, inda suka gudanar da bincike kan matakan da za a yi amfani da shi wajen nomawa kamar ciyawa, da bayar da tazara, kare kwari da cututtuka, ta yadda za a bunkasa yawan amfanin da zai samar, ba kuma tare da sauya yanayin halittar gadonsa ba.
Mburu ya ce, wannan masarar da aka yi bikin kaddamarwa a wannan rana, iri ne na cikin gida, kuma an gudanar da bincike ne kawai kan ayyukan da suka shafi noma, wadanda za su taimaka wajen samar da amfanin gona mai inganci. Haka kuma iri ne dake girma sosai a yankunan da ba a samun ruwan sama sosai.
Mburu ya ce, an shuka masarar ce, a watan Mayu a wani wurin gwajin noma na zamani dake kusa da cibiyar binciken hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka (SAJOREC) dake JKUAT, haka kuma masarar ta girma a lokacin da ya dace, inda aka samu kilogram 2,700 kan kowa ce Eka a yankin na gwaji, kimanin kaso 50 cikin 100 fiye da na abin da aka samu a kewayen yankin.
A cewar SAJOREC, jami’ar ta kebe Eka 10 na fili a matsayin wani babban yanki da za a gudanar noman gwaji, kana cibiyar nazarin kimiya ta kasar Sin, ta bayar da kudaden gudanar da aikin, da albarkatun da ake bukata gami da taimakon fasaha. Sassan biyu sun kuma shiga yin aikin tare da raba sakamakon binciken kimiyar noman da aka samu.(Ibrahim)