Masana kimiyya na kasar Sin sun samu gagagrumar nasara wajen kandagarkin cututtukan da ake samu daga sauro ta hanyar samar da wani tsarin na fasahar zamani dake bayar da jagoranci wajen dakile cututtuka.
Tawagar masana karkashin Chen Xiaoguang, shehun malami a jami’ar nazarin aikin likitanci ta kudancin Sin wato Southern Medical University ce ta samar da wannan fasahar sa ido da bibiya da aka fara amfani da ita a yankuna da dama na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin.
- Jiragen Saman NAF Sun Kai Hari Kan Taron ‘Yan Bindiga 400 A Zamfara
- ‘Yan Ta’addar ISWAP Sun Kashe Shugaban Mafarauta A Borno
Tsarin sa ido mai inganci na da muhimmanci, duba da cewa cututttuka kamar Chikungunya na yaduwa ne ta hanyar cizon sauro nau’in Aedes.
Chen Xiaoguang ya bayyana cewa, dabarun da aka saba amfani da su na yaki da sauro suna da tasgaro. Ya ce tarko da gidan sauro na kama sauro ne marasa shan jini, yayin da tsarin kama sauro cikin mazubi da ruwa, ke kama sauro masu jan jini da yin kwai.
Ya kara da cewa, abun da suka kirkiro na’ura ce dake gudanar da ayyuka biyu a lokacin da ake ciki, kuma tana da matukar inganci wajen sa ido da bibiyar sauro. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp