Masana a bangaren ilimi sun yabawa muhimmiyar rawar da Sin ke takawa wajen inganta ilimi mai inganci a nahiyar Afrika.
Yayin wani taron karawa juna sani na hadin gwiwa a bangaren ilimi tsakanin Sin da Afrika da ya gudana ranar Juma’a a birnin Addis Ababa na Habasha, masana sun jinjinawa kasar Sin bisa kokarinta na inganta ilimi mai inganci ta hanyar tallafin karatu, da koyar da sana’o’i da fasahohi ga dalibai ‘yan Afrika, da bayar da kudin samar da kayayyakin da ake bukata a cibiyoyin ilimi dake fadin nahiyar.
- An Kaddamar Da Bikin Nuna Kayayyakin Fasahohin Al’adu Masu Alaka Da Gasar Olympics A Shanghai Na Sin
- Gidajen Adana Kayan Tarihi Na Sin Sun Karbi Masu Ziyara Biliyan 1.29 A Shekarar 2023
Da yake tsokaci, Bonaventure Rutinwa, mataimakin shugaban jami’ar Dar es Salaam ta kasar Tanzania, ya ce kasar Sin na goyon bayan bunkasa matakin ilimi ga ‘yan Afrika, musammam ga mata da yara da matasa, kuma tana ci gaba da samar da ilimi mai inganci ta hanyar shirye-shiryen tallafin karatu da na bayar da horo daban-daban.
Shi kuma Samuel Kifle, shugaban jami’ar Addis Ababa, ya bayyana irin namijin kokarin da Sin ke yi wajen bunkasa kwarewa domin taimakawa yara da matasan nahiyar samun ingantaccen ilimi. Ya kuma bukaci gwamnatoci a Afrika su yi koyi da Sin, wajen samar da ma’aikata masu kwarewa da ilimi da shiga kirkire-kirkire da raya kimiyya da fasaha. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)