Cibiyar nazarin fasahar sadarwa ta kasar Sin ta bayyana cewa, an samu bunkasa sosai a fannin kere-keren fasahar kirkirarriyar basira (AI) ta kasar Sin, inda yawan kamfanonin bangaren ya zarce 5,300 a watan Satumba, wanda ya kai kashi 15 cikin 100 na dukkan adadin na duniya baki daya.
Mizanin kudin masana’antar ya zarce yuan biliyan 900 (kimanin dalar Amurka biliyan 126.7) a shekarar 2024, inda aka samu karuwarsa da kashi 24 cikin dari a ma’aunin shekara-shekara.
Bangaren fasahar AI na kasar ya kafa cikakken tsarin masana’antu wanda ya kunshi tun daga kan kayayyakin aiki da ake bukata, zuwa fasalin abubuwan da za a aiwatar, da kuma manhajojin aikace-aikacen masana’antu.
Cibiyar ta kara da cewa, kayayyakin manhajoji na zahiri da ake kerawa wadanda ake ganin ayyukansu a wayoyin hannu, da kwamfutoci da motoci masu amfani da fasahar AI suna samun ci gaba cikin sauri. (Abdulrazaq Yahuza Jere)