Tun daga farkon shekarar bana, ake ci gaba da kyautata matsayin masana’antun kasar Sin, yayin da masana’antun kere-keren fasahohin zamani ke ci gaba da bunkasa cikin sauri, wanda ya kasance jagora ga saurin sauye-sauye da kyautatuwar tattalin arzikin kasar.
Alkaluman da hukamar kididdigar kasar kasar Sin ta fitar na nuna cewa, a watan Oktoba, darajar masana’antun kere-keren fasahohin zamani na kasar, ta karu da kashi 10.6% bisa makamancin lokaci na bara, kuma saurin karuwar ta kai kashi 1.3% bisa na watan Satumba, lamarin da ya taimakawa ci gaban masana’antun kasar cikin sauri.
Tun daga farkon shekarar bana, ana kiyaye sauya da ma inganta masana’antun kasar, musamman ma yadda ake ci gaba da kyautata sassan masana’antun kasar zuwa na zamani kuma ba tare da gurbata muhalli ba, wanda ya kara azama kan bunkasar tattalin arzikin Sin sosai.
Xu Shaoyuan, mataimakin shugaban sashen nazarin tattalin arzikin sana’o’i na cibiyar nazarin harkokin bunkasuwa ta majalisar gudanarwar kasar Sin, ya ce sakamakon kokarin da ake yi da jarin da ake zubawa, ya sa aka aza harsashi mai inganci ta fuskar masana’antun kasar, kana kamfanoni suna kara samun kwarin gwiwa, suna da karfin samun ci gaba.
Masana’antun kere-keren fasahohin zamani sun zama ginshikan jagorantar sauyawa da kyautatuwar tattalin arzikin kasar Sin da kuma ci gaban kasar mai inganci. (Safiyah Ma)