Babban taron kungiyar kawancen habaka amfani da kimiyya da fasaha a aikin gona ta Sin da Afirka (CAASTIA) na shekarar 2025 ya fara gudana jiya Litinin a Addis Ababa, babban birnin Habasha, tare da mai da hankali kan hadin gwiwar samun wadatar abinci da zamanantar da aikin gona a Afirka.
Da take jawabi a taron, shugabar Cibiyar Kimiyya ta Afirka Lise Korsten ta bayyana cewa, kasar Sin ta nuna kwarewa a fannin noma mai yawan yabanya, wanda ake gudanarwa bisa fasaha, inda hakan ya sa ta iya ciyar da kusan kashi 20 cikin dari na yawan al’ummar duniya da kasa da kashi 9 cikin dari na fadin kasar noma a duniya. A halin yanzu, Afirka na fuskantar matsalar karancin abinci duk da cewa ita ce ke da kashi 60 cikin dari na fadin kasar noma da ba a nomawa a duniya.
Korsten ta kara da cewa, “Wannan sabanin na kason fadin kasa da yawan jama’a ya nuna bukatar yin hadin gwiwa mai daidaito: wanda zai hade damar da Afirka ba ta da amfani da ita tare da sabbin kirkire-kirkire na kasar Sin don gina tsarin samar da abinci na duniya mai dorewa.”
A nasa bangaren, shugaban ofishin jakadancin Sin a kungiyar Tarayyar Afirka (AU) Jiang Feng ya ce, kasar Sin a shirye take ta sanar da kwarewarta a fannin ci gaban noma da rage talauci a karkara ga kasashen Afirka don samun ci gaba na bai-daya.
Jiang ya kara da cewa, “Hadin gwiwar aikin gona tsakanin Sin da Afirka yana sauyawa daga tsohon yayi na bayar da tallafi zuwa hadin gwiwa mai dorewa da horaswar inganta kwazo. A wannan shekarar, gwamnatin kasar Sin ta sanar da manufar soke dukkan haraji na kayayyaki ga kasashen Afirka 53 wadanda ke da alakar diflomasiyya da ita. Wannan zai karfafa samun damar shigar da kayayyakin noma na Afirka zuwa kasuwar kasar Sin sosai.” (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
 
			




 
							








