Mista Balew Demissie, shaihun malami a jami’ar birnin Addis Ababan kasar Habasha, kana mai bincike a cibiyar nazarin manufofi ta kasar, ya ce hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ya jure sauye sauye cikin tsawon lokaci a tarihi, tare da haye tarin kalubale.
Mista Demissie, wanda ya bayyana hakan yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai ta Xinhua a kwanan baya, ya ce duk da irin sauye sauyen yanayin tafita a cudanyar kasa da kasa, Sin da kasashen Afirka sun ci gaba da alaka tare.
- Rikicin Masarautar Kano: Sarki Bayero Ya Ƙaddamar Da Sabunta Ginin Fadar Nassarawa
- Rundunar ‘Yansandan Jihar Kebbi Ta Ƙarawa Jami’ai 52 Muƙami
Malamin wanda ya yi tsokacin gabanin taron FOCAC na bana dake tafe nan da ‘yan kwanaki, ya bayyana hadin gwiwar Sin da Afirka a matsayin alakar da ta jurewa dukkanin wahalhalu, ta kuma kafu tun tsawon lokaci, tare da ci gaba da karfafa, yayin da sassan suka sha fama da kalubalen mulkin mallaka. Ya ce kawance na ‘yan uwantaka tsakanin Sin da Afirka ya samo asali ne daga kamanceceniyar tarihi, da martaba juna, da bunkasar hadin gwiwa.
Ya ce ya yi imani burin Afirka na zamanantarwa, zai ci gajiya daga Sin ta fuskar kara zuba jari a muhimman ababen more rayuwa a nahiyar, da rarraba kwarewa da kasashen nahiyar ta fuskar sarrafa hajojin masana’antu, da musayar fasahohi a sassan raya ayyukan gona, da makamashin da ake iya sabuntawa, da bangaren sanin makamar aiki ta fuskar ilimi da kiwon lafiya da dai sauran su. (Mai fassara: Saminu