Kasar Sin za ta gudanar da taron kolin mata na duniya a ranakun Litinin 13 da Talata 14 ga watan nan na Oktoba a birnin Beijing. Taron dake da babbar ma’ana ta fannin tabbatar da alkawarin Sin game da inganta hakki da moriyar mata a fadin duniya.
An bayyana hakan ne a cikin makala da masanin dangantakar kasa da kasa dan asalin kasar Kenya mai suna Adhere Cavince ya rubuta, wadda aka wallafa a jiya Jumma’a, babbar jaridar “The Star” ta kasar Kenya.
Makalar ta bayyana cewa, tun daga shekarar 1949, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, tana ta dora muhimmanci sosai kan harkokin mata, kuma karfafa kare hakki da moriyar mata, sun zamo cikin ayyukan inganta zamanantarwa na tsarin gurguzu, wanda ya haifar da babban sauyi ga bunkasar harkokin mata.
Nasarorin da kasar Sin ta samu a cikin gida, sun kafa ginshikin jagorancin duniya, wajen samar da ci gaban harkokin mata, musamman ta hanyar fitar da darussa, ta hanyar kyautata mu’amala tsakamnin bangarorin biyu. Babban misali shi ne yadda ake samun bunkasar dangantakar mata tsakanin kasashen Kenya da Sin, wadda aka inganta yayin ziyarar aiki da shugaban Kenya William Ruto ya kai kasar Sin a watan Afrilun bana. Kasashen biyu sun yi alkawarin zurfafa mu’amalar al’adu, ciki har da mu’amalar mata da matasa bisa tsarin dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. Wadannan matakai sun kunshi fannoni kamar su tallafin karatu da horar da sana’o’i, kuma dukkansu sun haifar da babban sakamako. (Safiyah Ma)