Daga ranar 22 zuwa 23 ga watan Maris, an gudanar da taron kasa da kasa karo na biyu kan “Demokuradiyya: Darajoji masu muhimmanci ga daukacin bil-Adama ” a nan birnin Beijing.
Darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin dake Najeriya, Charles Onunaiju ya shaidawa manema labarai a wurin taron cewa, cikakken tsarin dimokuradiyya da yake damawa da dukkan jama’a a kasar Sin, wata babbar nasara ce da jama’ar kasar Sin baki daya suka cimma karkashin jagorancin JKS. Demokuradiyya ce da ke mai da hankali kan jin dadin jama’a, da nufin ci gaba da inganta yanayin rayuwarsu.
Charles Onunaiju ya ce, a Afirka, muna mai da hankali sosai kan tsarin demokuradiyya da mulkin demokradiyya wanda ke jaddada dokoki, amma ba a mayar da hankali wajen taimaka wa mutane tunkarar kalubalen rayuwa. “Ina fatan dukkan kasashe, musamman kasashe masu tasowa na Afirka, za su nazarci cikakken tsarin demokuradiyyar jama’ar kasar Sin da ya kunshi jama’a a dukkan matakai, kuma su fahimci cewa, demokuradiyya ba wai kawai ta kunshi ka’idojin aiki ba ne, har ma da bukatar biyan hakikanin bukatun jama’a.”
A yayin taron, mamban hukumar kare hakkin dan Adam ta kasar Uganda Kugiza Kaheru, ya shaidawa manema labarai cewa, daukacin tsarin demokuradiyyar kasar Sin ya samo asali ne daga tushen tarihin al’adu, kuma jigonsa shi ne ci gaba da koyo, da ci gaba da koyi daga sauran sassa, da ci gaba da daidaitawa, da raya kasa, da kuma samun bunkasuwa bisa sauyi da zamani. Demokuradiyyar kasar Sin ba ta da tsauri da ra’ayin mazan jiya, amma tana da kyau wajen daidaita bukatun al’umma. Ba kawai a ka’idance ba ce, amma a aikace.
Shugaban jam’iyyar gurguzu ta kasar Zambiya, Dr Fred M’membe ya shaidawa menama labarai a yayin da yake halartar taron cewa, a kasar Sin, kana iya ganin cikakken darajar tsarin demokuradiyya, wato nuna damuwa da jin dadin bil-adama da kuma nuna damuwa ga mafi yawan jama’a, ba wai kawai masu sukuni ba.
Akwai attajirai da yawa a kasar Sin, amma ba masu arziki ne suke tsara manufofin gwamnatin kasar ba, amma bisa muhimman muradun al’ummar Sinawa. (Ibrahim Yaya)