• English
  • Business News
Thursday, May 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masarautar Bauchi Ta Tuɓe Rawanin Sanata Kan Sukar Gwamna Bala

by Khalid Idris Doya
9 months ago
in Labarai
0
Masarautar Bauchi Ta Tuɓe Rawanin Sanata Kan Sukar Gwamna Bala
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Masarautar Bauchi ta sanar da warware rawanin ‘Mujaddadin Bauchi’ da ta naɗa wa Sanatan da ke wakiltar mazaɓar Bauchi ta Kudu, Shehu Buba Umar bisa sukar gwamna Bala Muhammad. 

Idan za a tuna dai a yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen kujerar shugabancin ƙananan hukumomi na jam’iyyar APC, Sanata Buba ya zargi gwamnan jihar da jefa jama’a cikin matsin rayuwa, inda ya ce gwamnatin jihar ce ke da alhakin ƙuncin rayuwa da ake ciki ba wai shugaba Tinubu ba.

  • AU Ta Naɗa Pantami Shugaban Tsara Manufofin Masana’antun Afrika Karo Na 4
  • Ambaliyar Ruwa: Mutane 16 Sun Rasu, 3,936 Sun Rasa Matsugunansu A Jigawa – SEMA

Ya zargi gwamnatin jihar da karɓar tallafin tirelolin shinkafa da taki amma ba ta raba wa jama’a kamar yadda gwamnatin tarayya ta umarta ba.

Sanatan wanda ke ƙoƙarin kare Tinubu daga sukar da gwamna Bala ya masa a kwanakin ba.

A wata wasiƙa daga masarautar Bauchi ɗauke da sa hannun Nasiru Musa, a madadin Sakataren Majalisar da ya fitar a ranar Laraba, ta nuna abin da ya faru tsakanin gwamnan da Sanata a matsayin rashin biyayya da cin zarafi don haka ta cimma matsayar janye ‘Sarautar Mujaddadin Bauchi’.

Labarai Masu Nasaba

‘Yansanda Sun Musanta Zargin Kai Wa ‘Yan Bindiga Abinci Ta Jirgin Sama A Kogi

’Yan Bindiga Sun Sace Mutane 200 A Mazaɓa Ta A Zamfara – Ɗan Majalisar Tarayya

Wasiƙar wacce aka aike wa Sanatan kai-tsaye ta ce, “Bayan gaisuwa da fatan kana lafiya. Bayan haka, a zaman Majalisar Masarautan Bauchi na yau 14 ga watan Agusta, 2024 ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Bauchi, ta yi nazari mai zurfi kan abubuwan da ya faru na rashin biyayya da cin zarafin Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi, wanda yin hakan ya saɓa wa irin tarbiyya da al’adan Masarautar Bauchi.

“Bisa wannan dalili majalisa ta janye sarautar da ta ba ka na Mujaddadin Bauchi.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: BauchiGwamnaMasarautar BauchiSanataSuka
ShareTweetSendShare
Previous Post

Ban Taɓa Karɓar Cin Hanci Ko Taɓa Ƙuɗin Ƙananan Hukumomi Ba – Shekarau

Next Post

Birtaniya Za Ta Wahala Idan Likitocin Nijeriya Suka Bar Kasar – Ministan Lafiya

Related

‘Yansanda Sun Musanta Zargin Kai Wa ‘Yan Bindiga Abinci Ta Jirgin Sama A Kogi
Labarai

‘Yansanda Sun Musanta Zargin Kai Wa ‘Yan Bindiga Abinci Ta Jirgin Sama A Kogi

4 minutes ago
Gabar ‘Yan Bindiga A Tsakaninsu Ta Kara Tsanani A Zamfara
Manyan Labarai

’Yan Bindiga Sun Sace Mutane 200 A Mazaɓa Ta A Zamfara – Ɗan Majalisar Tarayya

2 hours ago
An Yi Wa ‘Yar Shekara 18 Fyade Har Lahira A Taraba
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Cafke Mutane 9 Kan Kisan Jigon Jam’iyyar PDP A Adamawa

3 hours ago
UTME
Manyan Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Maka JAMB A Kotu Biyo Bayan Samun Mummunan Sakamako A UTME

11 hours ago
Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa  Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista
Labarai

Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa  Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista

12 hours ago
gaza
Labarai

Kasafin Kudi Na Naira Tiriliyan 1.78 Na Abuja Ya Tsallake Karatu Na Biyu A Majalisa

13 hours ago
Next Post
Birtaniya Za Ta Wahala Idan Likitocin Nijeriya Suka Bar Kasar – Ministan Lafiya

Birtaniya Za Ta Wahala Idan Likitocin Nijeriya Suka Bar Kasar - Ministan Lafiya

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Musanta Zargin Kai Wa ‘Yan Bindiga Abinci Ta Jirgin Sama A Kogi

‘Yansanda Sun Musanta Zargin Kai Wa ‘Yan Bindiga Abinci Ta Jirgin Sama A Kogi

May 15, 2025
Gabar ‘Yan Bindiga A Tsakaninsu Ta Kara Tsanani A Zamfara

’Yan Bindiga Sun Sace Mutane 200 A Mazaɓa Ta A Zamfara – Ɗan Majalisar Tarayya

May 15, 2025
An Yi Wa ‘Yar Shekara 18 Fyade Har Lahira A Taraba

’Yansanda Sun Cafke Mutane 9 Kan Kisan Jigon Jam’iyyar PDP A Adamawa

May 15, 2025
UTME

ASUU Ta Yi Barazanar Maka JAMB A Kotu Biyo Bayan Samun Mummunan Sakamako A UTME

May 14, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

May 14, 2025
Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa  Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista

Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa  Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista

May 14, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

May 14, 2025
gaza

Kasafin Kudi Na Naira Tiriliyan 1.78 Na Abuja Ya Tsallake Karatu Na Biyu A Majalisa

May 14, 2025
Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa

Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa

May 14, 2025
Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa

Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa

May 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.