Majalisan Masarautan Zazzau karkashin Jagoranci Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR ta bayar da umurnin Koran Malam Sama’ila Abubakar Rimin Tsiwa Daya daga cikin Dogaran Fadan Zazzau daga aiki a Masarautan Zazzau.
Wata matashiya wanda take shirin Aure tazo Fadan Zazzau domin a sadata da Mai Martaba Sarkin Zazzau bisa neman taimako kan batun auren ta sai ta gabatar da bayanan ta ga Malam Sama’ila wanda maimakon gabatar da ita zuwa inda ya kamata, sai ya yaudareta zuwa wani wuri dabam inda shi da Abokansa suka yi lalata da ita.
Majalisan Masarautan Zazzau, ta umurci Rundunan ‘Yan Sanda da ta gaggauta kamalla bincike, kuma su gabatar da masu laifi cikin gaggawa a gaban Kotu domin yanke masu hukuncin dai-dai da laifinsu.
Haka kuma, Majalisan Masarautan Zazzaun ta dauki alkawarin bin sahun wannan batu domin tabbatar da an kwatanma wannan Matashiya hakkinta.
Walilin kafofin yada labarai na masarautar ta Zazzau Malam Abullahi Aliyu Kwarbai ya tabbatar da hakan a wata takarda da ya sanyawa hannu.
A halin yanzu jama’a ke tayin Allah wadai da faruwan wannan lamarin tare da Jan hankalin yan’mata masu zuwa wajan manya neman taikako.
Malama Sumayya Sa’ad Funtuwa yayin da take baiyana ra’ayinta ga wakilinmu akan lamarin cewa tayi, iyaye su kula tare da baiwa yaransu shawsra gami da yadda zasu rike lalura ta talauci da ake fama da shi a wannan lokacin tace hakan nada gayan muhimmanci.
Ita ko Malama Rabi Ibrahim Samaru cewa yayi idan Bera na da laifi to daddawa ma na da laifi don haka itama budurwan akwai inda take da laifi .
Malama Rabi ta kara da cewa da ya bata kudi masu yawa da babu Wanda zai ji su bisa haka tace tsoron Allah shine yake magance fasadi tsakanin mace da namiji a kowani hali.
Karshe tayi addu’ar Allah ya tsare mana zuriyarmu baki daya.