Wani rahoton masana’anta da aka fitar yau Juma’a ya bayyana cewa, masu amfani da intanet a kasar Sin sun kai yawan biliyan 1 da miliyan 100 zuwa Disamban 2024, inda adadinsu ya karu da miliyan 16.08 daga na bara.
Rahoton wanda cibiyar yada labarai a kan al’amuran intanet ta kasar Sin ta fitar, ya kuma bayyana cewa intanet ya yadu a sassan kasar Sin da kashi 78.6 bisa dari a shekarar 2024, yayin da aka cika shekaru 30 da sada kasar da hanyoyin sadarwar intanet na duniya.
A halin yanzu kasar Sin ce ke habaka kayayyakin amfani da intanet mafiya yawa a duniya, wadanda suke kunshe da fasahohi na zamani da kuma bunkasa ci gaban tattalin arzikinta na bangaren intanet cikin hanzari, kamar yadda rahoton ya bayyana. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)