Tawagar masu binciken kimiyya na kasar Sin sun gano wani nau’in kwayar halitta wato gene da ke kara yawan shinkafa, wanda ke da muhimmanci wajen samar da amfanin gona mai yawan gaske, a cewar jami’ar aikin gona ta Huazhong.
Shi dai wannan nau’in kwayar halitta na GY3 na iya kara yawan hatsi a kowace sanda kuma yana kara yawan amfanin gonar shinkafa da kusan kashi 10 cikin dari ta hanyar daidaita sinadarin cytokinin.
Sakamakon binciken ya nuna cewa, ana iya amfani da GY3 don yawan amfanin gona na shinkafar indica.
An wallafa binciken kwanan nan a yanar gizo a cikin mujallar Nature Genetics. (Mai fassara: Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp