Wasu masu binciken kimiyya na kasar Sin sun yi nasarar kera wani dan karamin mutum mutumin hannu bisa fasahar 3D mai tsayin micrometers 40, wanda kuma ke da kaurin da bai kai na gashin bil’adama ba, da za a iya amfani da shi wajen kamowa, da kuma sauyawa kananan kwayoyin halitta wuri.
Wata makala da aka wallafa cikin mujallar binciken kimiyya ta “International Journal of Extreme Manufacturing”, ta ce dan karamin hannun zai taka muhimmiyar rawa yayin gudanar da gwaje-gwajen farko-farko, da na tabbatar da sakamako na hakika a aikin likitanci, musamman duba da karuwar bukatar iya sarrafa kwayoyin halitta da kananan halittu masu rai.
Masu binciken na fatan mutum mutumin hannun zai taimaka wajen sarrafa kananan kwayoyin halittu, da gabatar da magunguna zuwa hakikanin sassan da ake bukatarsu yayin ayyukan jinya, da magance wasu larurori na muhalli. (Saminu Alhassan)