Darakta Janar na hukumar masu yi wa kasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa masu NYSC cewa, nan bada jimawa ba za a fara biyan mafi karancin albashi na N77,000.
Da yake jawabi a Abuja lokacin da ya kaddamar da motar bas din ma’aikata da kamfanin inshora na Capital Express ya bayar, DG ya ce an kammala shirye-shiryen kara musu alawus-alawus.
- NYSC Ta Mayar Da Sansaninta Na Bauchi Zuwa Kwalejin Kangere
- Cece-kuce Kan Badaƙalar Kuɗaɗe A NNPCL: SERAP Ta Bukaci Mele Kyari Ya Yi Bayani
Ya tabbatar musu cewa, abin da ya sa a gaba shi ne tsaro da jin dadin su, don haka a shekarar 2025 za su samu duk wasu alfanu da ya kamata.
Ahmed ya bayyana cewa, an samar da motar bas ɗin ne don sauƙaƙe matsalolin sufuri ga ma’aikatan hukumar.