Alkaluman da hukumar kididdigar fina-finai ta kasar Sin ta bayar, sun nuna cewa, yawan kudin da aka samu a bangaren fina-finan da aka gabatar a lokutan bikin hutun murnar ranar kafuwar jamhuriyyar jama’ar Sin na 2025 ya kai RMB yuan biliyan 1.835 kwatankwacin fiye da dala miliyan 25.74. Kana yawan masu kallo ya kai fiye da miliyan 50.07, kuma kashi 98.93% na kudin shigar, ya fito ne daga fina-finan da Sinawa suka tsara.
Zuwa ranar 8 ga Oktoba, jimillar kudin shiga na fina-finai a shekara ta 2025 ya kai yuan biliyan 43.789, kwatankwacin fiye da dala biliyan 6.1 wanda ya karu da kashi 18.98% idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.
Sakamakon bincike na gamsuwar masu kallon fina-finan Sinawa na bikin murnar ranar kafuwar sabuwar kasar Sin a shekarar 2025 ya nuna cewa, fina-finan sun samu yabo sosai da maki 85.4, wanda ya karu da maki 2.1 idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata, kuma shi ne mafi yawa a cikin shekaru hudu da suka gabata. (Amina Xu)
 
			




 
							







