Wasu masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa sun yaba wa Super Falcons bisa bajintar da suka nuna a gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA ta shekarar 2023, wanda kasar Australiya da New Zealand suka dauki nauyi.
Tawagar Nijeriya dai ta yi rashin nasara ne da ci 2-4 a bugun daga kai sai mai tsaron gida da Ingila a zagaye na 16, bayan da suka tashi 0-0 a filin wasa na Brisbane.
Wani bangare na masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa, wadanda suka zanta da NAN, sun bayyana cewar, Super Falcons sun bayyana cewar su ‘yan Nijeriya ne sabida jajirce akan abin da suke nema duk da kaddara ta riga fata.
Shugaban hukumar kwallon kafa ta FCT, Mouktar Mohammed, ya ce duk da cewa ‘yan wasan kasar sun yi rashin nasara a wasansu da kasar Ingila, amma sun nuna jajircewa matuka.
Masu horar da Super Falcons sun nuna cewa harkar kwallon kafar Mata a Nijeriya na samun tagomashi sosai.
Akalla kashi 70 cikin 100 na ‘yan wasan dole ne a ajiye su wuri guda, yayin da za a iya saka sabbin yan wasa a cikin tawagar domin maye gurbin wadanda suka tsufa, inji shi.