• English
  • Business News
Wednesday, October 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masu Sa Ido Sun Bukaci INEC Ta Sake Nazarin Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Kaduna

by Yusuf Shuaibu
3 years ago
Zaben Gwamnan Jihar Kaduna

Gamayyar masu saka ida a zaben 2023 sun bukaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), da ta sake yin nazari kan sakamakon zaben Jihar Kaduna.

Masu saka idon kan zabe dai sun ce zaben ya yi kyau a Jihar Kaduna, amma a wajen tattara sakamakon zaben bai yi daidai da abin da aka dora a safin INEC ba.

  • Shehu Sani Ya Yi Wa DSS Shagube Kan Zargin Kafa Gwamnatin Wucin Gadi

Jami’in kula da zaben gwamnan Jihar Kaduna, Farfesa Lawal Bilbis, ya bayyana cewa dan takarar jam’iyyar APC, Uba Sani ya samu kuri’u 730,002, inda ya doke abokin takararsa Isah Ashiru na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 719,196.

Jimillar sakamakon ya nuna cewa APC ta samu nasara a kananan hukumomi goma da suka hada da Zariya, Kaduna ta Kudu, Kaduna ta Arewa, Birnin Gwari, Giwa, Sabon Gari, Igabi, Ikara, Kauru, da Kubau, yayin da PDP ta lashe kananan hukumomi 13 na Makarfi, Kachia, Chikun, Kagarko, Jaba, Jama’a, Kaura, Zango Kataf, Soba, Kudan, Chikun, Kaura, Sanga da Lere.

A wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, babban jami’in cibiyar kula da da’a da dabi’u na kasa, Roman Azubuike, wanda ya yi magana a madadin jami’in hukumar INEC, ya ce ya kamata hedkwatar INEC ta kasa ta sake duba sakamakon zaben gwamnan Kaduna.

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta

Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal

“Muna kira ga INEC da ta sake duba sakamakon zaben gwamnan Jihar Kaduna.
“Zaben ya kasance a bayyane har zuwa lokacin fara tattara sakamakon zabe al’amura suka fara canzawa. Tun farko dai tsarin ya kasance a bayyane, amma a Kudancin Kaduna da Birnin Gwari da wasu kananan hukumomi ya kamata a sake yin nazari a kansu saboda ba a tura sahihin sakamakon zaben zuwa shafin INEC a kan lokaci ba.
“Don haka muna amfani da wannan dama wajen yin kira ga INEC da ta sake duba sakamakon zaben, musamman zaben gwamna,” Azubuike ya bayyana.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta
Da ɗumi-ɗuminsa

ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta

October 22, 2025
Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal
Labarai

Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal

October 22, 2025
Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe
Manyan Labarai

Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe

October 22, 2025
Next Post
Ku Dakata Da Gine-Gine A Filayen Gwamnati Da Makarantu – Abba Gida-Gida

Ku Dakata Da Gine-Gine A Filayen Gwamnati Da Makarantu - Abba Gida-Gida

LABARAI MASU NASABA

ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa

ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa

October 22, 2025
ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta

ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta

October 22, 2025
Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal

Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal

October 22, 2025
Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe

Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe

October 22, 2025
Gobara Ta Tashi A Kasuwar Alaba Da Ke Legas

Gobara Ta Tashi A Kasuwar Alaba Da Ke Legas

October 22, 2025
Gwamnoni Sun Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Fashewar Tankar Mai A Neja

Gwamnoni Sun Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Fashewar Tankar Mai A Neja

October 22, 2025
Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 

Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 

October 21, 2025
Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da Karfin Iska A Karkashin Ruwa

Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da Karfin Iska A Karkashin Ruwa

October 21, 2025
Aikin Jinya Kyauta: Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Zagaye Na 10 Na Kula Da Marasa Lafiya 3,447

Aikin Jinya Kyauta: Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Zagaye Na 10 Na Kula Da Marasa Lafiya 3,447

October 21, 2025
Ci Gaban Kasar Sin Ya Shaida Cewa Yawan Jama’a Ba Dalili Ne Na Rashin Ci Gaba Ba

Ci Gaban Kasar Sin Ya Shaida Cewa Yawan Jama’a Ba Dalili Ne Na Rashin Ci Gaba Ba

October 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.