Da Safiyar wannan ranar Juma’a an wayi gari da zanga-zangar lumana da masu sana’ar Gurasa suka gudanar don nuna damuwarsu kan hauhawar farashin Fulawa wanda hakan ke yin barazana ga Sana’ar ta su.
Hajiya Fatima, ita ce shugabar kungiyar masu sana’ar gasa Gurasa a Kano, ta yi wa manema labarai jawabi a lokacin da suke tsaka da gudanar zanga-zangar, ta ce yanzu haka kaso sama da 70% na masu wannan sana’a sun hakura da ita saboda tsadar Fulawa, ta bayyana cewa kullum suka je sayen Fulawa sai sun samu karin kudin da ya kama daga 1,500 zuwa sama.
Fatima ta ce a cikin ‘yan watannin da suka gabata suna sayen buhun Fulawa a kan kudi Naira 15,000 amma yanzu buhun Fulawar ya kai Naira 45,000 duk daya. wanda hakan yasa da yawa daga cikin masu wannan sana’ar suka hakura da ita.