Hauwa Habeeb Saleh Daliba a Jami’a da take burin samun sahihin ilimi gami da ganin ta tsaya da kafarta wajen sana’a domin dogaro da kanta, a cikin tattaunawarta da wakiliyarmu BILKISU TIJJANI KASSIM, ta bayyana irin gwagwarmayar dake cikin karatu da irin ya dace dalibi ya kasance a lokacin da yake zuwa makaranta. A karshe kuma ta ba wa mata shawarar kada su da jahilci, sannan kuma su kaucewa zaman banza su tashi tsaye domin neman na kansu, kamar dai yadda za ku karanta kamar haka:
Da fari za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki?
Suna na Hauwa Habeeb Saleh ina zaune a Garin Malam Madori dake Jihar Jigawa dake Karamar Hukumar Hadaijia na yi karatuna a Garin Malam Madori.
Kina Da aure?
A a ba ni da aure muna sa rai dai in sha Allah
‘Yar kasuwace ko ma’aikaciya ce?
A’a bana sana’a ina so dai na fara in Allah yarda, saboda yanzu karatu nake
Ya gwagwarmayar karatu ?
Alhamdulillah sanin kowa ne an san karatu akwai wahala sai an daure gashi nan gwagwarmaya muna ta fama sai dai fatan alkhairi da nasara Allah ya bamu sa’a.
Mene ne matakin karatun ki ba?
Ina aji daya a jami’a ne
Wanne irin addu’a ce idan aka yi miki kike jin dadi?
Idan aka ce Allah ya yi min albarka da kuma samin nasara a rayuwa ina jin dadin addu’ar nan
Wanne irin goyon baya kike samu daga wajen iyaye da ‘yan uwanki?
A gaskiya iyayena su ne karfin gwiwata domin suna goyan bayana akan karatuna da kuma harkokin rayuwa.
Kawaye fa?
Kawaye na suma suna goyan baya na sosai
Me kika fi so a cikin kayan sawa da kayan kwalliya? kayan sawa na fi son atamfa kayan kwalliya kuma Lip gloss
A karshe wacce irin shawara za ki ba ‘yan uwanki mata?
Ina ba wa ‘yan uwana mata shawara akan mu tsaya mu yi karatu, sannan kada mu yi zaman banza mu kama sana’a don za ta taimaka mana a zaman rayuwarmu Allah ya bamu sa’a.