Gimbiyar Dange, Barista Sa’adat Yunusa Muhammad, ta bayyana cewa mata, musamman waɗanda ke riƙe da muƙaman gargajiya, na taka muhimmiyar rawa wajen ci-gaban al’umma ta fuskar tarbiyya, da ilimi, da haɗin kai, da bunƙasa tattalin arziƙi.
Ta bayyana hakan ne a lokacin da Mai Girma Sarkin Bauran Dange, Alhaji Bello Usman, ya naɗa ta a matsayin Gimbiyar Dange ta farko a wani biki na musamman da aka gudanar a ƙaramar hukumar Dange, cikin Daular Usmaniyya, a ranar Asabar.
- Fahimtar Sabon Tunani: Samar Da Wadata Ga Dukkan Jama’a Ta Daidaita Gibin Dake Tsakanin Hamshakai Da Matalauta
- Ƙarfin Niyyar Manzon Allah (SAW) Da Matakinsa Na Aƙlul A’ala
A cikin jawabinta bayan naɗin, Barista Sa’adat ta ce wannan sarauta ta ba ta ƙarin ƙwarin gwuiwa wajen hidimtawa al’umma, musamman wajen tallafawa mata da matasa. Ta ce, “Sarautar nan ba karramawa ce kawai ba, kira ne na hidima. Idan muka tallafawa mata daga ilimi zuwa sana’o’i, mun tallafawa al’umma gaba daya.”
Ta ƙara da cewa, fitowarta daga zuriyar Shehu Usmanu Dan Fodiyo ta zame mata babban abin alfahari, tana mai tuna rawar da Nana Asma’u ta taka wajen ilimantar da mata da bunƙasa shugabanci a zamanin Mujaddadi. Ta ce wannan tarihi ne da ya tabbatar da cewa mace ba ta da iyaka idan aka ba ta dama.
A yayin bikin, Sarkin Bauran Dange ya kuma naɗa mijinta, Barista Ahmad Muhammad Musa, a matsayin Mayanan Dange, wanda shi ma sabon matsayi ne a masarautar. Ya ce an zaɓi ma’auratan ne bisa gudunmuwar da suke bayarwa wajen cigaban yankin da al’ummarsa.
Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, wanda Kwamishinan Ruwa, Alhaji Aminu Dodo Iya, ya wakilta, ya jaddada cewa sarautun gargajiya su ne ginshiƙin zaman lafiya da ci-gaban al’umma. Ya ce shugabannin gargajiya na taka rawa wajen haɗa kan jama’a da gwamnati, tare da tabbatar da ɗorewar cigaba a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya.











