Matar Shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, a ranar Asabar ta ce, bai kamata a yi watsi da mata ba, maimakon haka ma ya kamata a ba su karin damarmaki a bangaren shugabanci da mulki domin ba su tasu damar wajen kyautata ci gaban Nijeriya.
Ta shaida hakan ne a Abuja lokacin kaddamar da littafin da matar shugaban hafson sojojin Nijeriya, Misis Salamatu Yahaya, ta rubuta mai suna: “Strengthening the NAOWA Narrative.”
- Remi Tinubu Ta Fara Aiki A Matsayin Uwargidan Shugaban Nijeriya
- Mijina Zai Mayar Da Duk ‘Yan Gudun Hijira Gidajensu – Oluremi Tinubu
Uwargidan shugaban, wacce ta samu wakilcin Sanata Nora Daduut, ta ce, “Akwai bukatar a sake nazarin damarmakin da ake bai wa mata a bangaren shugabanci. Kuma wannan littafin zai taimaka sosai ba kawai wajen inganta rayuwar mambobin NAOWA ba, har ma ga illahirin matan Nijeriya ma.”
Tun da farko a jawabinta, mawallafiya kuma shugabar kungiyar matan sojoji (NAOWA), Salamatu Yahaya, ta ce, an rubuta littafin ne domin sake bude wa mata ido a bangaren shiga a dama da su a bangaren mulki da shugabanci kuma da alfanun da hakan ke da shi wajen samar da ci gaba mai ma’ana.
“Muhimmancin rawar da mata ke takawa a bangaren shugabanci baya misaltuwa saboda akwai hanyoyin da gudunmawar mata ke da hanzarin kawo ci gaba. Don haka gudunmawar su zata taimaka wajen bunkasar ci gaba a kasar nan.” Cewarta.