A yayin da Babban Zaben 2023 ke kara karatowa, jam’iyyar PDP a Jihar Sakkwato ta bayyana cewar dimbin mata za su fito su yi wa jam’iyyar ruwan kuri’a domin tabbatar da nasarar ta a dukkanin matakai.
Mataimakiyar shugaban kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar PDP a jihar, Farfesa A’isha Madawaki Isah, ce ta bayyana hakan a yau Talata a wajen taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar na kananan hukumomin Gada da Goronyo a ofishin jam’iyyar a Sakkwato.
- ‘Yansanda Sun Cafke Dan Shekara 16 Kan Zargin Cin Zarafin Mai Mala BuniÂ
- Buhari Ya Ba Ni Tabbacin Za A Gudanar Da Sahihin Zabe A 2023 – Atiku
Farfesa Madawaki, wadda kuma ita ce Kwamishinar Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, ta bayyana cewar a bisa ga cikakken goyon bayan da jam’iyyar PDP ta samu a jihar da bunkasa rayuwar mata da daukacin al’umma; mata za su fito kwansu da kwarkwata su zabi PDP daga sama har kasa baki daya.
‘Yar siyasar ta bayyana cewar gwamnatin Tambuwal ta aiwatar da muhimman ayyuka masu tasiri wadanda suka bunkasa rayuwar mata, kawar da matsalolinsu da inganta jin dadinsu tare da ba su muhimman mukamai sama da kowace gwamnati a jihar.
“Za mu gudanar da yakin neman zabe tun daga rumfuna, gida-gida da kofa-kofa domin kara godiya ga ‘yan uwanmu mata kan goyon bayan da suke bai wa wannan gwamnatin tare da kara bayyana masu muhimmancin zaben PDP tun daga sama har kasa baki daya.”
A jawabinsa, shugaban kwamitin yakin neman zaben PDP, Tsohon Ministan Sufuri, Honarabul Yusuf Sulaiman, ya bayyana cewar jam’iyyar adawa ta APC za ta zama tarihi a zaben 2023.
Ya ce al’ummar Jihar Sakkwato za su jagoranci kakkabe mulkin APC daga sama har kasa ta hanyar tabbatar da Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasa da Malam Sa’idu Umar a matsayin Magajin gwamna Tambuwal tare da zaben dukkanin ‘yan takarar PDP baki daya.