Mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kuma mataimakin firaministan majalisar gudanarwar kasar Sin He Lifeng, ya bayyana cewa, kasar Sin ta zama kasa ta biyu mafi girma a kasuwar kayayyakin masarufi a duniya. Baya ga kasancewarta babbar kasuwar kasa mai tasowa.
A shekarar 2022, jimillar darajar kayayyakin masarufi da aka sayar, ya kai yuan triliyan 44, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 6.4, karuwar kashi 7.9 bisa 100 a cikin shekaru goma da suka gabata.
He Lifeng ya bayyana haka ne, yayin bude bikin baje kolin kayayyakin masarufi na kasa da kasa karo na uku, da aka bude a birnin Haikou na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin jiya Litinin.
Ya kara da cewa, domin samun ci gaba, kasar Sin za ta mai da hankali kan kara samar da kayayyaki da ayyuka da hidimomi masu inganci, da tallafawa kamfanoni don karfafa bincike da ci gaba, da karfafa sabbin hanyoyin amfani da su, da inganta tsarin samar da kayayyakin masarufi. (Ibrahim)