Mataimakin firaministan kasar Sin kuma jagoran tawagar Sin a shawarwarin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, He Lifeng ya gana da sakatariyar harkokin kudin Amurka Janet Yellen a jiya a nan birnin Beijing, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra’ayoyi game da aiwatar da ayyukan da shugabannin Sin da Amurka suka cimma daidaito kansu a taron tsibirin Bali, da yanayin tattalin arziki da hada-hadar kudi na kasashen biyu da na duniya, da hada gwiwa wajen tinkarar kalubalen duniya da sauransu, shawarwarin dake da babbar ma’ana.
A ganin bangaren Sin, fadada fannonin kiyaye tsaron kasa zai kawo illa ga mu’amalar tattalin arziki da cinikayya yadda ya kamata. Haka kuma, Sin ta bayyana ra’ayinta, inda ta ce tana damuwa kan matakan Amurka na kayyade kamfanoninta. Bangarorin Sin da Amurka sun amince da kara yin hadin gwiwa wajen tinkarar kalubalen duniya baki daya, da kuma kiyaye mu’amala a tsakaninsu. (Zainab)