Mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida, ya nesanta kansa da sanarwar da jam’iyyar adawa ta PDP ta fitar na neman a miƙa ragamar mulkin jihar biyo bayan gwamnan jihar na shirin tafiya aikin Hajji 2024.
Tun da farko dai jam’iyyar PDP ce ta fitar da sanarwa a ranar Laraba 5 ga watan Yuni a Birnin Kebbi inda ta buƙaci Gwamnan Jihar da ya miƙa ragamar mulki ga mataimakinsa tun da yana shirin tafiya Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana.
PDP ta kafa hujja da sashe na 190(1)(2) na kundin tsarin mulki.
- Wata Hajiyar Jihar Kebbi Ta Rasu A Makkah, Shugaban NAHCON Ya Yi Ta’aziyya
- Matar Gwamnan Kebbi Ta Gudanar da Bikin Ranar Tsaftar Jinin Al’ada Ta Duniya A Argungu
A martanin da mataimakin Gwamnan, Sanata Umar Abubakar-Tafida ya mayar, ya ce ko da yaushe Gwamnan Jihar yana mika mulki ga mataimakinsa ko da tafiyar yini ɗaya ya yi ba ya jihar.
A cewar Sanata Umar, “Mun yi mamakin da’awar da ƴan adawa ke yi na cewa a miƙa min ragamar mulki, domin ko da rana ɗaya Gwamna Nasir bai taɓa hanani yin aiki ba”
In ji mataimakin Gwamna Abubakar- Tafida a yayin taron manema labaru da ya kira a gidansa da ke Birnin Kebbi.