Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Hon. Muhammad Samaila Bagudo, ya shaki iskar ‘yanci daga sansanin ‘yan bindiga bayan sun tsare shi na tsawon kwanaki da dama.
A cewar majiyoyin da ke kusa da Mataimakin Shugaban Majalisar, ya dawo gida ne da misalin karfe 8 na dare a ranar Asabar, cikin koshin lafiya kuma ba tare da wani rauni ba.
Wannan lamari ya haifar da farin ciki a Bagudo da sauran sassan jihar, inda mazauna yankin suka fara yin tururuwa zuwa gidan Mataimakin Shugaban Majalisar don jajantawa da kuma maraba da shi.
Ana sa ran Mataimakin Shugaban Majalisar zai gana da gwamnan Jihar, Dr. Nasir Idris, a safiyar yau Lahadi.
Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, babu wata sanarwa a hukumance daga hukumomi kan yadda Mataimakin Shugaban Majalisar ya kuɓuta.














