Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng a yau Asabar ya gabatar da jawabi a dandalin tattaunawar zaman lafiya na duniya karo na 12 a nan birnin Beijing, inda ya yi kira ga hadin gwiwar inganta harkokin tsaron duniya, da kiyaye daidaito da adalci, da kuma sa kaimi ga hadin gwiwar tsaron kasa da kasa. Ya kuma bayyana cewa, duniya na fuskantar manyan sauye-sauye da ba a taba ganin irinsu ba a cikin karni guda, Mista Han ya kara da cewa, kasar Sin a matsayinta na mamba ta dindindin a kwamitin sulhu na MDD, kuma kasa mai muhimmanci a cikin kasashe masu tasowa na duniya, za ta ci gaba da kasancewa a kan tafarkin da ya dace a duniya mai cike da sauye-sauye. (Mai fassara: Yahaya)