A ranar 8 ga watan Satumbar nan ne aka bude bikin baje kolin zuba jari da cinikayya na duniya na kasar Sin karo na 25 a birnin Xiamen, inda kusan shugabannin kamfanoni na kasashe mabambanta da shugabannin cibiyoyin zuba jari na kasa da kasa guda 100 suka zo kasar Sin.
A wata zantawa da aka yi da shi, mataimakin shugaban kamfanin Unilever Zeng Xiwen, ya shaida wa wakilin kafar CCTV News cewa, tun ba yau ba gwamnatin kasar Sin tana jaddada kudurin bude kofa ga kasashen waje, lamarin da ya bai wa kamfanoni tabbaci. Kasuwar kasar Sin tana da girma, kirkire-kirkiren da ake yi na da karfi, kuma manufofin da ake tsarawa suna gudana babu tangarda. Domin zama “mai tseren gudun fanfalaki” a kasar Sin, ya kamata Unilever ya ci gaba da zurfafa kafa ressansa a cikin kasar, da kuma rungumar damarmakin da ake samu a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp