A yayin taron manema labaru da aka gudanar a yau, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta mayar da martani kan ra’ayoyin da ministar cinikayyar kasar Amurka ta yi a kwanakin baya, kan matakan Amurka na kayyade fitar da mattarar bayanai ta microchip zuwa kasar Sin, tana mai cewa, kasar Sin ta riga ta sha bayyana ra’ayinta kuma Sin ta yi imanin cewa, matakan Amurka za su kawo illa ga moriyar kamfanonin Sin, har ma ga kasuwar samar da kayan ta duniya baki daya. Wannan ya sabawa ka’idojin tattalin arzikin kasuwanci da yin takara cikin adalci, kuma bai dace da moriyar kowane bangare ba, Sin tana adawa da wannan mataki.
Hakazalika kuma, Mao Ning ta bayyana cewa, ra’ayin ba da kariya ga cinikayya zai hana musayar kayayyaki, da hidimomi, da zuba jari da sauransu, kuma zai kawo illa ga farfado da bunkasar tattalin arzikin duniya. Wani abin damuwa shi ne, wasu kasashe sun yanke hulda da sauran kasashe bisa dalilin kiyaye tsaro, wannan batu zai kara kawo wa duniya rashin tsaro da hadari. (Zainab)