Ranar 21 ga wata, fadar White House ta kasar Amurka ta kaddamar da takardar bayani ta manufar zuba jari mai mayar da Amurka a gaba da komai, inda ta sanar da kyautata manufar kasar kan harkokin zuba jari.
A cikin manufar, an bayyana cewa kebe fannonin da za a haramta wa Sin da Amurka su zuba jari, abu ne mafi muhimmanci, wanda za a kara takaita zuba jarin. Matakin, wanda ya yi gamin-gambiza da batun tsaron kasa wuri guda, ba komai ba ne illa nuna wariya sannan ya yi hannu riga kwata-kwata da tsarin kasuwanci, yana kuma matukar kassara hadin gwiwar tattalin arziki da harkokin kasuwanci na yau da kullum a tsakanin kamfanonin Sin da Amurka.
- Zan Fice Daga APC Matuƙar Abdullahi Abbas Ya Ci Gaba Da Zama Shugaba A Kano – Ministan Tinubu
- Ƴansandan Katsina Sun Kwato Mutum 13 Daga Hannun Masu Garkuwa
Kasar Sin ta ce, ta riga ta sa ido kan matakin Amurka, kuma za ta dauki wajababbun matakan kiyaye halastattun hakkokinta.
Shin wane irin sakamako za a samu bayan da Amurka ta takaita harkokin zuba wa juna jari? Masharhanta sun yi nuni da cewa, matakin Amurka ya saba wa ka’idojin kasa da kasa kan harkokin zuba jari, da cinikayya, da tattalin arzikin kasuwanci, sannan ya bata sunan ita kanta, kana ya cutar da moriyar kanta da damammakin kamfanoninta. Lalle Amurka tana cutar da wasu da ita karan kanta.
Ba wanda zai hana kasuwa ta ci gaba da gudana. Sannan kamfanonin Sin da Amurka suna matukar sha’awar hada kansu. Bugu da kari, neman samun moriyar juna da samun nasara ga ko wane bangare, zabi ne mafi dacewa da su. Don haka, ya zama tilas Amurka ta yi taka-tsan-tsan kan takaita zuba wa juna jari da kuma ingiza raba-gari da Sin. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp