Duk da yadda jagoran yankin Taiwan Lai Ching-te ya sha rokon neman tausayi da lalama, Amurka ta kara harajin kwastan kan yankin.
Kwanan nan, kasar Amurka ta sanar da sabon jerin sunayen kasashe da yankuna da ta sanya wa “harajin fito na ramuwar gayya”, inda ta kakaba harajin 20% a kan yankin Taiwan na kasar Sin. A daidai lokacin da ake damuwa cewa irin wannan babban harajin zai yi matukar tasiri ga masana’antun Taiwan, gwamnatin Lai Ching-te ta baiwa kanta hakuri, har ma ta ce wai daidaita yawan harajin na “wani dan lokaci” ne, kuma ta samu nasara a wannan matakin. Game da haka, jama’a a yankin sun soki gwamnatin Lai Ching-te kan yadda ta makance wajen biye wa Amurka, tare da cin amana da lalata Taiwan, lamarin da ya sa al’ummar yankin ke biyan farashi mai tsada.
- Gwamnatin Sin: Gwamnatin Jama’a Domin Jama’a
- Manoma Sun Caccaki Tinubu Kan Ƙarfafa Shigo Da Shinkafa Da Masara Daga Ƙasashen Waje
Ta abin da ake kira “harajin fito na ramuwar gayya”, mutane sun sake gani a fili cewa, a idon Amurka, Taiwan ganima ce da take amfani da ita wajen cimma burikanta. Abin da ake kira dangantakar abokantaka tsakanin Amurka da Taiwan da gwamnatin Lai Ching-te ta yi ta yadawa, ba komai ba ne.
Bisa rahoto daga kafofin watsa labarun waje, Lai Ching-te ya jinkirta shirin sa na ziyara ba bisa ka’ida ba ga wasu kasashen Latin Amurka da yake kira “kasashen diflomasiyya” a watan Agustan, saboda gwamnatin Amurka ta ki amincewa da bukatarsa ta yada zango a kasar.
Wasu manazarta sun bayyana cewa, a halin yanzu, yana da matukar muhimmanci ga Washington ta ci gaba da yin shawarwari da tuntubar Sin kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Kuma gwamnatin Amurka ba ta son ganin Lai Ching-te ya kawo tsaiko ga shirin, don haka take tafiyar da harkokin da suka shafe shi da sanyin jiki.
Wannan kuma ya tabbatar da cewa, gwamnatin Lai Ching-te a zahiri ‘yar dara ce a hannun Amurka, wadda za ta iya amfani ko watsi da ita. (Mai fassara Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp