Ba wani abu da ke tabbatar da rashin gamsuwa da manufofin Amurka don gane da Isra’ila, sama da yadda sojin Amurka Aaron Bushnell ya cinnawa kan sa wuta a gaban ofishin jadancin Isra’ila dake Amurka.
Aaron Bushnell mai shekaru 25 da haihuwa, ya hallaka kan sa ta wannan mummunar hanya, wanda a cewar shafin yanar gizo na “Politician”, hakan alama ce dake nuna karuwar fusatar jami’ai dake cikin gwamnatin Amurka ita kan ta.
- Sin: Abun Da Aka Sa Gaba Shi Ne Farfado Da Zaman Lafiya
- Sin Ta Kira Taron Tattauna Kan Rahoton Gwamnati
A cewar wani abokin Bushnell, kwana guda kafin ya kunnawa kan sa wuta, Bushnell din ya sanar da shi wasu sirrika da suka shafi aikin sojin Amurka, ciki har da yadda sojojin na Amurka ke da hannu dumu dumu wajen kisan kiyashin da ake yiwa Falsdinawa.
Rahotanni daga kafofin watsa labaran Amurka na cewa, tun wajen farkon watan Oktoban bara ne gwamnatin Amurka ta tura dakarun musamman zuwa Isra’ila.
Zanga-zangar da wannan matashin soja ya gudanar ta hanyar sadaukar da ran sa, ta jefa sako kunnuwan ‘yan siyasar Amurka, wanda ke cewa “Kar ku ci gaba da take hakkokin al’umma ta fakewa da “hakkin dan Adama”. Lokaci ya yi da ‘yan siyasar Amurka za su yi karatun ta nutsu, su kuma dawo cikin hankulan su. (Mai fassara: Saminu Alhassan)