A kwanan nan, kasar Amurka ta sanar da sanya karin harajin kwastam da ya kai kaso 10% kan kayayyakin da kasar Sin ke fitar da su zuwa kasuwannin Amurka. Wannan mataki ya keta ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, wanda kuma zai lalata huldar dake tsakanin Sin da Amurka a fannin cinikayya. Yanzu haka, kasar Sin ta ce za ta kai kara ga kungiyar WTO, gami da daukar matakan da suka wajaba wajen kare moriyarta.
A ganin kwararru masu nazarin al’amuran duniya, dalilin da ya sa sabuwar gwamnatin kasar Amurka daukar matakin nan na sanya karin haraji shi ne domin neman tilastawa sauran kasashe su biya kudi, ta yadda kasar Amurka za ta samu damar sassanta matsalar tattalin arziki da take fuskanta. Sai dai an ce matakin zai sa jama’ar kasar Amurka kashe karin kudi wajen sayen kayayyakin masarufi, da rasa dimbin guraben aikin yi.
A nata bangare, matakin da Amurka ta dauka zai sa yawan harajin kwastam da ake kakabawa kayayyakin da kasar Sin ke fitar da su zuwa Amurka kaiwa kimanin kaso 30. Amma hakan ba zai yi tasiri sosai kan tattalin arzikin kasar Sin ba, saboda tun tuni kasar ta fara daidaita manufar fitar da kayayyakinta. Yanzu haka, yawan kayayyakin da Sin take fitarwa zuwa Amurka ya riga ya ragu zuwa kasa da kaso 15%, cikin dukkan kayayyakin da Sin ke fitar da su kasuwannin ketare.
Ban da haka, matakin da kasar Amurka ta dauka na sanya karin harajin kwastam bai shafi Sin kawai ba, wanda shi ma ya jibanci kasashen Mexico da Canada, wadanda suka tabbatar da cewa za su sanya karin haraji kan kayayyakin kasar Amurka don mayar da martani ga matakin Amurka. (Bello Wang)