Dr. Doyin Abiola, matar marigayi Cif Moshood Kashimawo Abiola, ɗan takarar zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993, ta rasu tana da shekaru 82.
Iyalanta sun tabbatar da cewa ta rasu da misalin ƙarfe 9:15 na daren ranar Talata, 5 ga watan Agusta, 2025.
- Remi Tinubu Ta Bai Wa Waɗanda Ambaliya Ta Shafa A Neja Tallafin N1bn
- Kwamishinan Sufuri Ya Yi Murabus Kan Belin Wani Da Ake Zargi Da Laifin Safarar Kwaya A Kano
Marigayiyar, ta kafa tarihi a kafar yaɗa labarai ta Nijeriya inda ta zama mace ta farko da ta riƙe muƙamin Manajan Darakta kuma Babbar editan jaridar ƙasa.
Ta fara aikin jarida ne a shekarar 1969 a Daily Sketch, inda shafinta na “Tiro” ya shahara wajen taɓo batutuwan al’umma, musamman kare haƙƙin mata.
A shekarar 1970, ta tafi Amurka don ƙaro karatu inda ta samu digiri na biyu a fannin jarida, kana ta dawo gida ta shiga aiki da jaridar Daily Times a matsayin marubuciya, kafin daga baya ta zama Babbar Editan Sashen Labaran Fasali, daga nan kuma ta samu digirin digirgir (PhD) a hulɗar jama’a da kimiyyar siyasa a 1979.
Ta sake kafa tarihi bayan da jaridar National Concord mallakar MKO Abiola ta naɗa ta a matsayin editan jaridar ta farko, inda A shekarar 1986, aka ɗaga darajarta zuwa matsayin Manajan Darakta kuma Babban Edita mace ta farko da ta riƙe wannan matsayi a tarihin jaridun Nijeriya.
Ta auri MKO Abiola a shekarar 1981, kuma ta tsaya tsayin daka tare da shi wajen gwagwarmayar siyasarsa da rikicin da ya biyo bayan zaɓen 12 ga watan Yuni, inda ta bayar da gagarumar gudunmawa a fagen jarida, tare da shafe kusan shekaru 30 tana jan ragamar kafafen yaɗa labarai a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp