Matar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Patience Jonathan ta kai wa Matar shugaban kasa Remi Tinubu ziyara a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Patience wadda ta kai ziyarar a ranar Laraba, ta danganta ziyarar a matsayin goyon baya ga Remi, inda kuma ta baiwa Remi tabbacin mara mata baya.
Ta kuma baiwa daukacin matan kasar nan tabbacin cewa, Remi Tinubu za ta janyo su a jiki, domin tabbatar da shirin Remi da ta kirkiro da shi da ake kira a turance Renewed Hope wanda zai kai ga nasara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp