Kwalejin koyar da ilmin gudanar da harkokin kasa ya kaddamar da ajin horas da matasa jami’an kasar Sin a lokacin bazara na 2024 a yau Juma’a da safe a nan birnin Beijing. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umurni, inda ya jadadda cewa, matasa jami’an Sin su kasance karfi mai inganci wajen raya sha’anin JKS da kasar, kuma za su sauke nauyin ci gaba da raya tsarin mulki na gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin nan gaba. Matasa jami’ai na da muhimman ayyuka a kan wuyansu nan gaba, suna da makoma mai haske, dole ne su nace ga riko da akidun jam’iyya na hakika da cika alkawarinsu, da kuma kokarin samun ci gaba don sauke nauyin dake wuyansu yadda ya kamata.
Ban da wannan kuma, karon farko ne an gabatar da littafin dake dauke da wasu bayyanan Xi Jinping game da kare hakkin bil Adama na harsunan Sinanci da Faransanci, kana kaddamar da taron tattaunawar basirar Sin a fannin daidaita harkokin hakkin bil Adama a duk fadin duniya a birnin Paris, hedkwatar Faransa a jiya Alhamis. Wannan littafi ya shigo da muhimman bayanan Xi Jinping kan yadda za a mutunta da kuma kare hakkin bil Adama. (Amina Xu)