Sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’a da cibiyar nazarin watsa labaran kasa da kasa a sabon zamani ta tattara, karkashin jagorancin kafar talabijin ta CGTN, dake karkashin rukunin kafofin watsa labarai na kasar Sin CMG, da jami’ar Renmin ta kasar Sin, albarkacin cika shekaru goma da gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya ya nuna cewa, matasa da shekarun haihuwarsu ke tsakanin 18 da 44, wadanda suka bayyana ra’ayinsu, sun amince matuka da muhimmin tunanin shawarar, kuma sun yaba matuka da sakamakon da aka samu, bayan gina shawarar a cikin shekaru goma da suka gabata.
Yayin kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka kada, an lura cewa, matasan da suka bayyana ra’ayinsu, kaso 84.6 bisa dari sun amince da “ruhin hanyar siliki” da kasar Sin ta gabatar, wato “hadin gwiwa cikin lumana, da bude kofa tare da yin hakuri, da koyawa juna fasahohi, da cin moriyar juna domin samun ci gaba tare” . Kaza lika, kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ta nuna cewa, matasa masu karancin shekaru sun fi amincewa da shawarar, yayin da a tsakanin matasan da shekarun haihuwarsu suke 18 zuwa 24, kaso 88.8 bisa dari sun amince da “ruhin hanyar siliki”.
Rahotanni sun bayyana cewa, an gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ne ga matasa 3,857 dake kasashe 35, wadanda suka kunshi Amurka, da Birtaniya, da Japan, da Afirka ta kudu, da Agentina, da Thailand, da Najeriya, da Peru, da Mexico da sauransu. (Mai fassara: Jamila)