Zababben gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya bayyana cewa, ba zai lamunta iyalansa su yi masa katsalandan acikin gudanar da gwamnatinsa ba.
Gida-Gida ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a bayaninsa jim kadan bayan hukumar zabe ta kasa INEC ta mika masa takardar shedar lashe zaben gwamna.
Zababben gwamnan ya bayyana cewa, mataimakinsa shima ba zai bari iyalansa su yi masa katsalandan wajen tafiyar da aikinsa a matsayin mataimakin gwamna ba.
Gida -Gida ya ce, babu gaba a siyasa, ina kuma kira ga dan takarar gwamna na APC a jihar Nasiru Gawuna da sauran ‘yan takarar gwamna na jihar da ba su samu nasara a zaben ranar 18 ga watan maris ba da su hada hannu da gwamnati don ciyar da jihar Kano gaba.
Daga karshe, zababben Gwamnan ya yi godiya ta musamman ga jami’an tsaro a jihar sabida gudunmawar da suka bayar wajen tabbatar da an kammala zaben cikin aminci da kwanciyar hankali.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp